Rivers: Fubara Ya ba da Mamaki da Ya Sake Maganganu kan Tinubu da Wike

Rivers: Fubara Ya ba da Mamaki da Ya Sake Maganganu kan Tinubu da Wike

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya ce matakin Bola Tinubu na saka dokar ta-baci a Jihar Rivers ya ceci jihar daga rikici da rugujewar gwamnati
  • Simi Fubara ya bayyana cewa ana bin tsarin sasanci da sulhu domin dawo da zaman lafiya da aiki tsakanin bangarorin gwamnati a jihar
  • Gwamna Fubara ya nuna kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba mulkin dimokiradiyya zai dawo da cikakken tsari a jihar Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Gwamnan Jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ya yaba da matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na saka dokar ta-baci a jihar.

Gwamna Simi Fubara ce matakin ya hana barkewar rikicin siyasa da zai iya durkusar da jihar gaba ɗaya.

Fubara
Fubara ya yaba wa Tinubu kan saka dokar ta baci a Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Rahoton Arise News ya nuna cewa Fubara ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudanar da shugabanni da magoya bayan tafiyarsa ta"Simplified Movement" a Port Harcourt.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ya ce yana da yakinin cewa gwamnatin jihar za ta dawo da cikakken aiki, inda bangaren zartaswa da na majalisa za su cigaba da hadin kai don ciyar da jihar gaba.

Gwamna Fubara ya yaba da zaman sulhu a Rivers

Fubara ya bayyana cewa an shiga wani mataki na zaman sulhu domin dawo da zaman lafiya da hadin kai tsakanin jiga-jigan siyasa a jihar.

Punch ta wallafa cewa Fubara ya ce akwai bukatar kowa ya sauko daga matsayinsa, ya rungumi juna da zuciya ɗaya don ceto jihar.

A cewarsa:

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne jihar ta ci gaba. Ba wai ni ko kai ba ne; jihar ce tafi muhimmanci. Dole ne mu yafi juna, mu sasanta."

Fubara ya ce Tinubu ya ceci jihar Rivers

Gwamnan ya bayyana cewa idan ba don matakin Tinubu ba, da lamarin jihar ya rikide zuwa wani mummunan rikici.

Ya gode wa shugaban ƙasa saboda irin basira da gaggawar da ya nuna wajen dakile rikicin tun kafin ya karu.

Fubara ya ce:

“Ina rokonku da ku gode wa Shugaba Tinubu. Ya dauki mataki ne da hikima kuma a lokacin da ya dace. Shi ne ya dakile rikicin. Da ba haka ba, da wani labarin ake yanzu,”

Rikicin Rivers: Fubara ya yaba wa Wike

Gwamnan ya ce yana fatan nan ba da jimawa ba, za a samu daidaito tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Ya bayyana cewa ana cigaba da gudanar da tarukan sulhu a Abuja, ciki har da wanda aka yi a gidan Wike.

Fubara ya ce:

“Babu dalilin da zai hana zaman lafiya tsakanina da oga na,”
“Za mu sasanta, kuma za mu cigaba da aiki tare.”

Fubara ya ce duk wani fushi ko ɓacin rai da wasu ke da shi ya kamata a maye gurbinsa da yafiya da hakuri don ceto jihar daga koma baya.

Rivers
Fubara ya ce zai yi sulhu da Wike. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

APC ta ce tana maraba da Simi Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ce tana maraba da gwamna Siminalayi Fubara idan zai sauya sheka.

Shugaban APC na jihar Rivers ne ya bayyana hakan, inda ya ce babu abin da zai hana jam'iyyar aiki da Fubara tare.

Baya ga haka, shugaban jam'iyyar ya ce za su mika ragamar APC ga gwamna Siminalayi Fubara da zarar ya sauya sheka zuwa cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »