Wike Ya Kasa Hakura da Kalaman Sule Lamido, Ya Yi Martani mai Zafi
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike bai ji daɗin sukar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi masa
- Wike wanda ya yi martani ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa ya ce Sule Lamido bai tsinanawa PDP komai ba
- Lere Olayinka ya bayyana cewa Wike mai bin doka da oda ne saɓanin tsohon gwamnan na jihar Jigawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Lere Olayinka, babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi wa Sule Lamido martani kan sukar ubangidansa.
Lere Olayinka, ya ƙaryata zargin da tsohon gwamnan na jihar Jigawa, ya yi na cewa Nyesom Wike ya aikata ba daidai ba wajen kulle hedikwatar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa martanin na hadimin Wike na cikin wata sanarwa ne da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sule Lamido ya caccaki Wike
Sule Lamido ya zargi Wike da zama annoba ga jam’iyyar PDP, inda ya nemi a kore shi daga jam’iyyar bayan hukumar FCTA ta kulle hedikwatar jam’iyyar PDP.
Hukumar FCTA ta kulle hedkwatar ne bisa rashin biyan kuɗin harajin fili da ya wuce shekaru 28, duk da faɗakarwa da aka dinga yi tun daga watan Satumban 2023.
Wane martani Wike ya yi?
Amma a cikin martanin da ya yi mai zafi, Lere Olayinka ya bayyana cewa Wike yana da cikakken biyayya ga doka, kuma ba zai lamunci zalunci ko cin zarafi ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
“Ministan Abuja, Nyesom Wike, ba mamba bane na ƙungiyar Sule Lamido ta rashin bin doka da oda. A wurinsa, kowa dole ne ya bi doka idan ana hulɗa da al’amuran birnin tarayya."
- Lere Olayinka
Ya ƙara da yin watsi da sukar da Sule Lamido ya yi, inda ya nuna cewa tsohon gwamnan bai tsinanawa PDP komai ba face kare muradun kansa na siyasa.
“Ba mu da lokacin yin gardama da mutumin da ke ɗaukar jam’iyyar PDP kamar ta tsaya ne a iya jihar Jigawa kawai, inda nan ne farkon jam’iyyar kuma nan ne ƙarshenta."
“Tun da ya bar ofis a matsayin gwamna a 2015, me PDP ta samar a Jigawa, idan ban da Sule Lamido da ƴaƴansa da ake tsayarwa takara?”
- Lere Olayinka

Asali: Facebook
Lere Olayinka ya jaddada cewa Wike yana da niyyar tabbatar da bin ƙa’idodin da suka shafi dokokin birnin Abuja, kuma ba zai tsaya yin cacar baki da Sule Lamido ba.
Wike da rikicin PDP
Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja a yanzu, yana kara zama babban jan aiki ga jam’iyyar PDP, kamar yadda wasu jiga-jigai a jam’iyyar ke nunawa.
Duk da kasancewarsa daya daga cikin gagarumin jiga-jigan jam’iyyar a baya, abubuwan da yake aikatawa yanzu suna kara jefa PDP cikin rikice-rikice da rashin jituwa.
Yanzu haka, wasu daga cikin 'yan jam’iyyar na kallon Wike a matsayin wanda ya ke ja da baya tare da hana jam’iyyar ci gaba, musamman ganin irin matakan da yake dauka da kuma kalaman da wakilansa ke yi.
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana Wike a matsayin “annoba” ga PDP, yana mai cewa yana da karfin iko fiye da yadda ake bukata.
Masu sharhi na ganin cewa Wike yana amfani da matsayin sa na Minista don nuna wa PDP karfi, yana daukar matakai da za su iya cutar da jam’iyyar a siyasance.
Rashin jituwa da wasu shugabanni, musamman game da kulle ofishin PDP, na kara nuna cewa Wike ba ya tafiya da ra’ayin jam’iyya gaba ɗaya. Wannan hali na iya kara durƙusar da PDP idan ba a shawo kan lamarin ba cikin gaggawa.
Sule Lamido ya yi maganar murƙushe ƴan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna illar da ke shirin murƙushe ƴan adawa.
Sule Lamido ya bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da wanzuwa ne idan PDP na nan da ƙafafunta domin ta zama wani ɓangare na tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa idan aka ruguza PDP, Najeriya za ta samu kanta ƙarkashin shugabanci na kama-karya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng