Matsaloli 5 da Hadakar 'Yan Adawa Za Ta Iya Fuskanta wajen Doke Tinubu
FCT, Abuja - Haɗakar jam'iyyun adawa domin kawar da Shugaba Bola Tinubu da APC a zaɓen 2027 na ci gaba da ɗaukar saiti a fagen siyasar Najeriya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jagororin haɗakar da suka haɗa da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Peter Obi na ci gaba da shirye-shiryen ganin sun dunƙule waje ɗaya don tunkarar zaɓen 2027.

Asali: UGC
Atiku ya sanar da kafa haɗaka don doke Tinubu
A ranar 20 ga watan Maris 2025, Atiku Abubakar ya sanar da kafa haɗakar ƴan adawa don tunkarar zaɓen shekarar 2027, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Manyan jagororin ƴan adawa da ke cikin haɗakar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Eufai da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaɓen 2023, Peter Obi.
Akwai buƙatar samar da haɗaka
Duba da yadda aka raunana jam'iyyun adawa, akwai buƙatar sun haɗe wuri ɗaya domin shiga zaɓen 2027 kansu a haɗe.
Dukkanin manyan jam'iyyun adawa na PDP, LP da NNPP na fama da rikice-rikicen cikin gida. Akwai yiwuwar cewa ba za su taɓuka abin kirki ba idan suka shiga zaɓen kansu a rarrabe.
Ƙalubalen da haɗaka za ta iya fuskanta
Duk da cewa ƴan adawa sun amince da haɗewa waje guda don tunkarar zaɓen 2027, akwai matsaloli da dama da za su iya fuskanta.
Ga wasu daga cikinsu nan a ƙasa:
1. Fitar da ɗan takara
Babban ƙalubale da haɗakar ƴan adawa za ta iya fuskanta shi ne fitar da ɗan takarar da zai fafata da Shugaba Bola Tinubu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ƙalubalen shi ne wa zai janye wani idan har shugabannin ƴan adawa suka haɗu a kan dandali ɗaya, ganin cewa duka Atiku Abubakar da Peter Obi na da niyyar tsayawa takarar shugabancin ƙasa.
Wasu na hasashen cewa Atiku zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da Peter Obi zai yi masa mataimaki.
Hakazalika Atiku ba zai yi wa Peter Obi mataimaki ba saboda an taɓa rantsar da shi har sau biyu a matsayin mataimakin shugaban ƙasan Najeriya.
Peter Obi yana ganin shi ne mafi shahara wanda tushen goyon bayansa daga Kudancin ƙasar nan zai ba haɗakar jam’iyyun karɓuwar da take buƙata don samun nasara.
2. Rashin samun masu samar da kuɗi
Ba kamar a 2015 ba, lokacin da aka samu manyan masu ɗaukar nauyi, wannan haɗakar jam’iyyun yanzu ba ta da irin wannan goyon baya.
Akwai fargaba cewa duk wanda suka zaɓa a matsayin ɗan takara, jam'iyya mai mulki na na iya rinjayarsa da kuɗi don ya zama ɗan amshin shata.
Hakazalika jam'iyya mai mulki na iya amfani wasu ƴan leƙen asiri su kutsa cikin jam’iyyar don lalata tsarin daga ciki.

Asali: UGC
3. Rashin samun goyon bayan gwamnoni
Wani babban ƙalubale ga haɗakar shi ne rashin samun cikakken goyon bayan gwamnoni, waɗanda ke da tasiri sosai a harkokin siyasa da kuma tabbatar da nasarar jam’iyya a jihohinsu.
Ya zuwa yanzu dai babu wani gwamnan da ya fito ya nuna cewa yana tare da haɗakar jam'iyyun ƴan adawa.
Hasalima gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, sun fito sun nesanta kansu da haɗakar, inda suka bayyana cewa ba za su shiga cikinta ba.
4. Fitar da jam’iyya
Akwai buƙatar tsara yadda za a fito da jam’iyyar da za ta zama dandalin haɗin gwiwar, domin samar da tsarin da zai ɗauki kowa da kowa ba tare da nuna fifiko ba.
Wasu rahotanni sun nuna cewa jagoroin haɗakar sun fitar da jam'iyyar ADC a matsayin wacce za su yi amfani da ita.
5. Tallata kansu ga ƴan Najeriya
Galibin jagororin haɗakar tsofaffin ƴan siyasa ne waɗanda suka taɓa riƙe madafun iko a ƙasar nan.
Wasu ƴan Najeriya na iya yi musu kallon cewa babu wani sauyi da za su kawo, kawai suna son karɓar mulki ne domin su ci ribar hakan tare da su da ƴaƴansu.
Dole ne ƴan haɗakar sun sauya masu irin wannnan tunanin ta hanyar tallata kansu ta yadda za a yi musu kallon sun sha bamban da masu riƙe da madafun iko a yanzu.
Tsohon sanata ya yi fatali da haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Mudashiru Husain ya yi watsi da yunkurin 'yan adawa na kafa haɗaka.
Tsohon sanatan mai wakiltar Osun ta Ƴamma a majalisar dattawa ya bayyana cewa ƴan adawan ba su da haɗin kan da ake buƙata domin samar da irin wannan tafiyar.
Ya kuma yi nuna da cewa babu wata haɗaka komai girmanta da za ta iya kawowa Shugaba Bola Tinubu cikas a zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng