Tsohon Sanata Ya Sare Gwiwoyin Atiku, El Rufai da Peter Obi kan Hadaka
- Tsohon sanata a jihar Osun, Mudashiru Husain ya yi fatali da haɗakar ƴan adawa don kofar da Shugaɓa Bola Tinubu a 2027
- Sanata Mudashiru Husain ya bayyana cewa babu wata haɗaka komai girmanta da za ta iya kawar da Tinubu a 2027
- Ya nuna cewa haɗakar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Peter Obi ba ta da wata alƙibla ta siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Tsohon Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma, Sanata Mudashiru Husain, ya yi magana kan haɗakar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Peter Obi.
Sanata Mudashiru Husain ya yi watsi da haɗakar yana mai cewa ƙawancen na su ba komai ba ne face hadin gwiwar masu buri mara inganci da ba zai iya kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba a 2027.

Asali: UGC
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu da kansa, kuma aka fitarwa manema labarai a ranar Lahadi a birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Me Mudashiru Husain ya ce kan haɗaka?
Mudashiru Husain ya ce ƙawancen na su ya rasa zurfin siyasa, haɗin kai da kishin ƙasa da ake buƙata domin samar da wani zaɓi da ya fi gwamnati mai ci a yanzu.
A cewarsa, Shugaba Tinubu cikin shekaru biyu kacal ya riga ya sanya Najeriya a kan tafarkin cigaba, wadda wannan nasarar, hatta masu suka sun fara amincewa da ita.
"Na ji ya zama wajibi na faɗi gaskiya. Babu wata haɗaka, komai girmanta da za ta iya cire Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga kan mulki."
“Mun ga fuskokin da muka saba gani, Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, da Babachir Lawal, duk sun haɗe guri guda. Manufarsu ɗaya ce, su kifar da mutumin da shugabancinsa ya fara sauya alƙiblar tattalin arziƙin Najeriya."
“Amma mu faɗi gaskiya. Me ya haɗa waɗannan mutane? Ba hangen nesa bane. Ba haɗin kai ba ne. Ba aƙidar siyasa ba ce."
"Abinda ya haɗa su shi ne buri, wanda akasari yana da nasaba da muradin ƙashin kai. Wadannan ba su ne ginshiƙan kafuwar sahihin madadin gwamnatin da ake da ita ba."
- Mudashiru Husain

Asali: Facebook
Tsohon sanata yace kawuna ƴan haɗaka sun rabu
Mudashiru Husain ya kuma yi nuni da rarrabuwar kawuna da rashin daidaito a cikin ‘yan adawar, yana mai cewa dagewar Peter Obi wajen tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar LP, na nuna cewa da wuya za samu haɗin kai.
Tsohon dan majalisar wakilai sau biyu kuma dan takarar gwamna a jihar Osun karkashin jam’iyyar APC ya kammala da bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa ƴan adawan ba za su iya girgiza Shugaba Tinubu ba gabanin zaɓen 2027.
Ƙusa a APGA ya ba Atiku shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban matasan jam'iyyar APGA na ƙasa, Eze-Onyebuchi Chukwu ya koma ba da shawara ga Atiku Abubakar.
Shugaban matasan ya shawarci Atiku Abubakar kan ya haƙura da burin sake tsayawa takara a zaɓen 2027.
Eze-Onyebuchi ya nuns cewa ya kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya goyi bayan matashi domin yin takara a 2027.
Asali: Legit.ng