Yan Jigawa Sun Jawo Rikici a Taron Haɗaka tsakanin Atiku, Obi da Jiga Jigan APC
- Taron hadin kan ‘yan siyasa a Abuja ya rikici bayan wakilan Jigawa sun fusata kan wanda za a ce ya wakilce su
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal ya bayyana wakili, sai wakilan Jigawa suka ki amincewa da wanda aka fitar
- Bayan dakile rikicin, Mustapha Lamido da wani wakili sun zama zababbun wakilai, yayin da jami’an tsaro suka kare manyan shugabanni da suka halarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An samu hatsaniya yayin da ake gudanar da taron haɗaka tsakanin jam'iyyun adawa a Abuja.
Taron hadin gwiwa tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dan LP, Peter Obi, da tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya dawo rikici.

Asali: Facebook
An samu hatsaniya a taron haɗakar Atiku, Obi
Lamarin ya faru ne a taron da ake gudanarwa a otal din Abuja Continental a yau Lahadi, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Taron wanda Kungiyar Tattaunawar Siyasa ta Kasa (Arewa) ta shirya, ya gamu da tsaiko daga daliget din jihar Jigawa.
Rigimar ta barke ne lokacin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana wanda zai wakilci Jihar Jigawa a wajen taron.
A cikin fushi, wasu daga cikin wakilan Jigawa suka mamaye wurin manyan baƙi a taron wanda ya sake dagula lamura da sanya fargaba a wurin.

Asali: Twitter
Taron haɗaka: Mustapha Lamido ya wakilci Jigawa
Mutanen sun hana wanda aka fitar ya yi magana, suna cewa ba za a wakilce su haka ba saboda ba a bi ka'idar da ta dace ba.
Yayin da rigimar ta tsananta, jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda, DSS, da masu gadi na musamman suka tsare da manyan baki da ke wurin.
An samu kwanciyar hankali bayan an yi ta roko domin samun maslaha da natsuwa a wurin taron.
Daga bisani, dan tsohon gwamnan Jigawa, Mustapha Lamido ya zama daya daga cikin wakilai kafin aka samu sauki.
Ƙoƙarin jam'iyyun adawa domin kifar da Tinubu
Hakan na zuwa yayin da jam'iyyun adawa ke ta kokarin nemo hanyoyin da za su kayar da Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Duk da kokarin da suke yi ana ci gaba da samun matsaloli nan da can saboda kowa daga cikin masu neman takara na da muradun da ya ke son cimmmawa.
Wasu majiyoyi sun ce jam'iyyun adawa sun amince su yi amfani da jam'iyyar ADC a matsayin inda za su hadu domin kawo karshen mulkin Tinubu a 2027.
An ba Atiku shawara kan takara a zaɓe
Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya samu shawara daga wajen jigo a jam'iyyar APGA mai alamar zakara.
Shugaban matasan APGA na ƙasa, Eze-Onyebuchi Chukwu ya buƙaci Atiku da ya haƙura da sake neman takarar shugaban ƙasa a 2027.
Jigon na APGA ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da Wazirin Adamawa zai goyi bayan matashi domin ɗarewa kan mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng