Segun Sowunmi Ya Haska wa Jam'iyyar PDP Hanya, Za a Kassara Tafiyar Atiku kafin 2027

Segun Sowunmi Ya Haska wa Jam'iyyar PDP Hanya, Za a Kassara Tafiyar Atiku kafin 2027

  • Segun Sowunmi ya ce lokaci ya yi da shugabannin PDP za su yi duk mai yiwuwa su dawo da tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi
  • Jigon PDP ya ce idan ka duba sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 kaɗai za ka gane jam'iyyar na bukatar dawo da tsohon gwamnan Anambra
  • Sowunmi ya ce tun da aka kammala zaɓen 2023, jam'iyyar PDP ta faɗa cikin rikici wanda har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jigon PDP, Segun Sowunmi, ya bayyana cewa lokaci ya yi da jam'iyyar za ta duba yiwuwar dawo da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi.

Peter Obi ya fice daga PDP ne a watan Mayun 2022, inda ya yi zargin cewa ana amfani da kudi da sayen kuri’u a lokacin zaben fidda gwani.

Peter Obi.
Sowunmi ya bukaci a lallaba Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da Channels tv, Segun Sowunmi ya ce lokaci ya yi da PDP za ta lallaɓa Obi ya dawo cikinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jigo ya shawarci PDP ta dawo da Peter Obi

Sowunmi na ganin ya zama dole PDP ta koma ta nemi Obi, musamman ganin yadda goyon bayan da yake samu daga matasa da masu kishin ƙasa ke kara karfi.

“Daya daga cikin ‘ya’yan PDP daga Kudu maso Gabas wanda ya bar jam’iyyar, saboda yana ganin an yi watsi da yankinsa, ya samu ƙuri'a miliyan 6.2 a zaɓen 2023.
"PDP ta faɗi zaɓe, ta nufi kotu an tabbatar mata da rashin nasara, duk mai hangen nesa, tunanin da zai fara yi shi ne taya za mu dawo da Peter Obi?"

- Segun Sowunmi.

Yadda PDP ta sha fama da rikicin shugabanci

Jam’iyyar PDP ta faɗa cikin rikici ne tun bayan kayen da ta sha a zaben shugaban ƙasa na 2023, inda Atiku Abubakar ya sha ƙasa a hannun shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Bayan sauke Iyorchia Ayu, an nada Umar Damagum a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyya na ƙasa.

Tun bayan wannan lokaci, Arewa ta Tsakiya ta fara matsa lamba cewa a bari ta ƙarasa zangon mulkin Ayu, lamarin da ya raba kawunan ƴaƴan PDP.

Har ila yau, rikici ya ƙara ɓarkewa kan kujerar sakataren PDP tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, wanda hakan ke kawo matsala wajen batun sauya shugabanci.

Segun Sowunmi.
Sowunmi ya ce Shugaba Tinubu ba abin raina wa ba ne domin yana da kwakwalwa Hoto: Segun Sowunmi
Asali: Facebook

Jam'iyyar PDP ta ruguza kanta da kanta

Sowunmi ya ƙara da cewa ƴan siyasa na tururuwar barin PDP zuwa APC saboda raunin da jam'iyyar ta yi kanta, wanda za a iya warwarewa tun da farko.

“Akwai matakin da idan aka kai za ka iya zargin abokan faɗa da laifi, amma idan gazawa ta zama ruwan dare, to ba za ka zargi kowa ba ka zargi kanta.
“Mutane da dama na kuskuren raina Bola Tinubu saboda lafiyarsa amma ina sanar da ku, kwakwalwarsa kamar ta ƙatuwar halitta ce. Duk wanda ya raina shi zai yi nadama,” in ji Sowunmi.

Ɗan SDP ya nuna alamun goyon bayan Peter Obi

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023 da ya gabata, Adewole Adebayo ya ce zai iya janyewa Peter Obi a 2027.

Adebayo ya ce ana ci gaba da tattaunawa don kafa haɗakar ƴan adawa da nufin kayar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Adebayo ya ce duk da har yanzu bai yanke shawara ba, yana yaba wa da irin yadda Peter Obi ke tafiyar da harkokinsa na siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »