Bukola Saraki Ya Dauko Hanyar Magance Matsalar PDP domin Bugawa da APC a 2027
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya gana da wasu jiga-jigan PDP a Enugu domin duba hanyoyin farfaɗo da jam’iyyar
- Taron ya samu halartar gwamnan Enugu, Peter Mbah, da sanata Seriake Dickson da Ibrahim Dankwambo, a ƙarƙashin kwamitin sulhu na PDP
- Abubakar Bukola Saraki ya ce sun tattauna matsalolin cikin gida tare da fara fito da ingantaccen tsari domin dawo da martabar jam'iyyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Enugu - A wani yunkuri na sake farfaɗo da jam’iyyar adawa ta PDP, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya jagoranci wata muhimmiyar ganawa a jihar Enugu.
Saraki ya gana ne tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar ƙarƙashin kwamitin sulhu da inganta makomar PDP a Najeriya.

Asali: Facebook
Ana son dinke barakar jam'iyyar PDP
Legit ta tattaro bayanai kan yadda ganawar a gudana ne a cikin wani sako da Saraki ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ganawar ta samu halartar gwamnan Enugu, Peter Mbah, da tsofaffin gwamnoni; Seriake Dickson na Bayelsa da Ibrahim Dankwambo na Gombe, wadanda dukkansu mambobi ne na kwamitin.
Saraki ya bayyana cewa sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka addabi jam’iyyar, tare da fara tsara sababbin matakai domin dawo da martabarta a siyasar Najeriya.
Saraki ya ce an fara nazarin matsalolin PDP
A cikin sakon da Saraki ya wallafa bayan taron, ya ce ba su yi biris da matsalolin da ke damun jam’iyyar ba, illa ma dai sun tsaya sun kalli matsalolin da idon samar da mafita.
Ya ce sun fara duba matakan gyara da za su farfado da tushe da kuma gina sabuwar sahihiyar hanya ta nasara.
Saraki ya bayyana cewa wannan yunkuri ba mai sauƙi ba ne, domin yana bukatar aiki tukuru da jajircewa daga kowane ɗan jam’iyyar da ke son ganin PDP ta dawo da martabarta.
Saraki ya ce PDP za ta iya dawo da martabarta
Saraki ya nuna cikakken imani da jam’iyyar PDP lura da matakan da ta taka baya, ya ce jam’iyyar na da damar dawo da martabar ta.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da aka yi zaman da shi yana wakiltar Gombe ta Arewa ne a Gombe bayan shafe shekarau yana mulkin jihar.

Asali: Facebook
Haka zalika yana cikin shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Gombe da ma yankin Arewa maso Gabas baki daya.
Ibrahim Dankwambo ya wallafa a Facebook cewa zaman da suka yi kamar sharan fage ne a kan taron jam'iyyar da suke shirin yi a watan Agusta a jihar Kano.
Ganduje ya ce PDP na fama da manyan matsaloli
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyyar PDP ta dawo tamkar maras lafiya mai fama da cutar numfashi.
Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyar APC da aka yi a fadar shugaban kasa.
Ganduje ya ce saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar ne wasu 'yan PDP ke sauya sheka zuwa APC domin samun mafita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng