Babban Malami Ya Tsunduma Siyasa, Ya Bayyana Kujerar da Zai Nema a Takarar 2027

Babban Malami Ya Tsunduma Siyasa, Ya Bayyana Kujerar da Zai Nema a Takarar 2027

  • Wani limamin coci daga jihar Kogi, Fasto Adejola Babagbemi ya bayyana aniyarsa ta neman zama ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Yagba
  • Babban limamin ya sanar da shirinsa na tsayawa takarar ne a wurin taron ƙaddamar da ƙungiyarsa, wanda aka haɗa da bikin ƙarin shekararsa a Abuja
  • Ya ce ya yanke shawarar fitowa takara ba don neman muƙami ba, sai don hidimtawa al'umma da kawo ci gaba a Yagba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani malamin addini dan asalin jihar Kogi, Fasto Adejola Babagbemi, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar ɗan Majalisar Wakilan Tarayya mai wakiltar Yagba a 2027.

Adejola ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da kungiyar GB IRORUN Movement, wadda ta kunshi manyan 'yan siyasa, kwararru da abokansa, a Abuja.

Adejola Babagbemi.
Limamin coci ya fito takarar ɗan Majalisar Tarayya a Kogi Hoto: Adejola Babagbemi
Asali: Facebook

Leadership ta ce, da yake hira da ƴan jarida bayan taron, malamin cocin ya ce al'ummar mazaɓarsa na bukatar shugabanci na gari, hangen nesa, tausayi da ƙwarewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Meyasa babban malamin ya tsaya takara?

Fasto Babagbemi, wanda ya kafa kuma jagoran ƙungiyar GB IRORUN, ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne domin haɗa kai da kuma kawo ci gaba a Yagba.

"Ina tsaye a gabanku yau ba don murnar ƙarin shekara kaɗai ba, sai don amsa kiran al'umma, kiran hidima, haɗin kai, jagorantar al'umma zuwa matakin ci gaba.
“Ba don kaina na fito takara ba, ko don mukami, sai dai na yi haka ne saboda jama’ata, manoma a Mopamuro, 'yan kasuwa a Yagba ta Gabas, dalibai da tsofaffi a Yagba ta Yamma.
"Burina shi ne a bai wa kowanne ɗan Yagba dama daidai gwargwado ba tare da nuna banbanci ba."

- Fasto Adejola Babagbemi.

Limamin cocin ya kara da cewa ya dade yana aikin wayar da kai a matakin ƙasa, aikin jin kai da kuma tallafa wa matasa.

Ya kuma bayyana cewa gogewarsa a fagen shugabancin addini, aiki gwamnati da na kamfanoni, da shiga hidimar jama'a sune suka sa ya ji ya shirya wakiltar al'umma a Majalisa.

Jihar Kogi.
Fasto Adejola Babagbemi ya ce yana da gogewar shugabanci Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Manyan mutane sun halarci taron malamin

Wannan taro dai ya kasance na kaddamar da kungiyar da kuma bikin zagayowar ranar haihuwar malamin, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Taron ya samu halartar magoya baya daban-daban, jiga-jigan siyasa, da abokan aiki, wadanda suka nuna goyon baya ga hangen nesan Fasto Adejola Babagbemi tare da yabawa ayyukansa na baya.

Fasto Babagbemi ya kuma yi kira ga daukacin mazauna Yagba, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, da su hada hannu wajen gina yankin kan tubalin adalci, cigaba da fata mai kyau.

"Gobenmu ta fara tun yau, kuma idan muka haɗa kai tare da Allah, da falala, da jajircewa, za mu cimma nasara,” in ji shi.

Fastocin Gwamna Makinde sun shiga Kano

A wani labarin, kun ji cewa matasa sun fara liƙa fastocin takarar shugaban kasar gwamnan Oyo, Seyi Makinde a wasu muhimman wurare a birnin Kano.

An ga fastocin a wuraren da jama’a ke hada-hada kamar kewayen filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), yankin Wapa da gadar Dangi.

Ƙungiyar matasan da ta liƙa fastocin ta bayyana cewa zuwa makon gobe, za su karaɗe jihohin Arewa domin tallata Gwamna Seyi Makinde.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »