2027: Abubuwan Sani kan ADC yayin da Atiku, El Rufai, Obi Suka Zabi Jam'iyyar Hadaka
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta zama sabuwar amarya a fagen siyasar Najeriya bayan da hankalin ƴan adawa ya koma kanta.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Shugabannin ƴan adawa sun amince da amfani da jam’iyyar a matsayin dandalin fafatawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Twitter
Ƴan adawa sun zaɓi ADC don haɗaka
Ƴan adawa da ke jagorantar kafa haɗakar fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, sun zaɓi jam'iyyar ADC a matsayin inda za su koma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Jagororin ƴan adawa da suka haɗa da Alhaji Atiku Abubakar (PDP), Peter Obi (LP), da Mallam Nasir El-Rufai (SDP), sun amince da yin ƙawance domin kawar da APC daga mulkin Najeriya a 2027, cewar rahoton Arise News.
A bisa hakan ne Atiku, Obi, El-Rufai sun amince su koma ADC, wadda za ta zama jam'iyyar dukkanin ƴan adawar da ke cikin haɗakar ganin bayan Shugaba Bola Tinubu da APC.
Abubuwan sani kan jam'iyyar ADC
A wannan rahoton mun yi nazari kan abubuwan da suka shafi jam'iyyar ADC tun daga kafuwarta da tasirinta a siyasar Najeriya.
1. Kafuwar ADC
Jam’iyyar ADC an kafa ta a shekarar 2005 ta hannun wasu masu fafutukar siyasa da ƴan Najeriya masu kishin sauyi. A baya an san jam'iyyar ne da sunan Alliance for Democratic Change a cewar bayanai daga shafin jam'iyyar na adcparty.com
Babban mutumin da ya jajirce wajen kafa ta shi ne Ralphs Okey Nwosu, wanda ke shugabantar jam’iyyar a matakin ƙasa tun kafuwarta.
Jam’iyyar na ɗaukar kanta a matsayin dandalin siyasa na tsaka-tsaki da ke goyon bayan shugabanci mai haɗa kai, ƙarfafa matasa da cigaban ƙasa.
2. Rajista da INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta yi wa ADC rajista a hukumance a shekarar 2006 a matsayin jam’iyyar siyasa.
3. Zaɓe na farko
ADC ta fara shiga babban zaɓe a shekarar 2007 inda ta tsayar da ƴan takara a muƙamai daban-daban a fadin Najeriya.
Sai dai har zuwa yanzu jam'iyyar ba ta shahara wajen lashe wasu kujeru ba.
4. Shugabannin ADC
- Shugaban jam'iyya na ƙasa - Chief Ralph Okey Nwosu
- Sakataren jam'iyya na ƙasa - Alh. Said Baba Abdullahi
- Ma'aji na ƙasa - Mr. Cavin Alagoa
- Sakataren kuɗi na ƙasa - Dr. Rislan Abdulazeez Kanya
- Shugaban matasa na ƙasa - Barr. Maurice Ebam
- Shugabar mata ta ƙasa - Hon. Mrs Kayauta Yakubu
5. Tasirin ADC a siyasar Najeriya
A shekarun da suka gabata, ADC ta shiga cikin zaɓuka da dama, inda ta tsayar da ƴan takarar shugaban ƙasa da na ƴan majalisu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
A zaɓen shekarar 2023, ADC ta zaɓi Dumebi Kachikwu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Duk da cewa ADC tana shiga zaɓukan shugaban ƙasa akai-akai, bata taɓa samun gagarumar nasara ba.
A zaɓen 2023, jam’iyyar ta samu ƙuri’u 81,919 inda ta zo ta biyar bayan Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP.

Asali: Twitter
A zaɓen 2019, ɗan takararta marigayi Dr. Obadiah Mailafia ya samu ƙuri’u 97,874 inda ya zo na hudu daga cikin ƴan takara 73.
A zaɓen 2015 kuma, Dr. Mani Ibrahim Ahmad ya tsaya takara inda ya samu ƙuri’u 29,666 ya zo na bakwai daga cikin ƴan takara 14.
A zaɓukan ƴan majalisar tarayya na 2023, Leke Abejide ya sake lashe zaɓe domin wakiltar mazaɓar Yagba a jihar Kogi a ƙarƙashin ADC da ƙuri’u 23,271, inda ya doke ƴan takarar APC da PDP.
Jam’iyyar ta kuma lashe wata kujera ta majalisar wakilai ta hannun Salman Idris daga Kabba-Bunu/Ijumu, Kogi, sai dai daga bisani ya sauya sheƙa zuwa APC.
Sanatocin PDP sun gindaya sharaɗin shiga haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP sun kafa sharuɗɗa domin shiga haɗakar neman kawar da Bola Tinubu da APC a zaɓen 2027.
Sanatocin na PDP sun bayyana cewa za su shiga haɗakar ne kawai idan ta kasance jam'iyyu ke jagorantar ta ba wasu ɗaiɗaikun mutane ba.
Sun bayyana cewa haɗakar za ta yi nasara ne kawai idan ta kasance tana a ƙarƙashin jagorancin jam'iyyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng