Tsohon Gwamnan Kano Ya Shiga Hadakarsu Atiku, Ana Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da wasu jiga-jigan 'yan siyasa czgz Arewa sun shiga hadakar 'yan adawa
- A wani taro na kwamitin hadakar da aka gudanar ranar Alhamis, an tsayar da ranar 30 ga Mayu domin yanke shawara kan jam'iyyar hadaka
- Rotimi Amaechi ne ke jagorantar kwamitin duba yiwuwar kafa sabuwar jami'iyyar hadaka, yayin da ake nazari kan amfani da SDP ko ADC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An dora wa tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, da takwaransa na Cross River, Liyel Imoke, alhakin yanke shawara kan jam'iyyar hadaka gabanin 2027.
Kwamitin hadakar na so Amaechi da Imoke su yanke shawarar ko kafa sabuwar jam'iyya ko kuma amfani da daya daga cikin jam'iyyun adawa domin yin takara a ciki.

Asali: Twitter
Tsohon gwamnan Kano ya shiga hadakar Atiku
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar 'yan siyasar Arewa (LND), Dr Umar Ardo, ya karanta, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Umar Ardo ya karanto sanarwar ne yayin da yake bayyana shirin ƙungiyar na shiga cikin wannan hadakar bayan taron da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis.
Taron ya samu halartar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, wanda shi ma aka ce ya shiga cikin hadakar, da wasu fitattun ’yan siyasa daga Arewacin ƙasar nan.
Wannan hadaka dai ta samu goyon bayan manyan ’yan adawa kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu da dama.
Masu hadaka na shirin kafa sabuwar jam'iyya
Da yake magana da manema labarai a Abuja, Dr Umar Ardo ya bayyana cewa Liyel Imoke ne ke jagorantar kwamitin nazari kan dacewar amfani da wata jam’iyyar adawa.
Yayin da ya ce an dora wa Rotimi Amaechi alhakin jagorantar kwamitin da zai duba dacewar yin rijistar sabuwar jam’iyya.
Jagoran LND ya bayyana cewa za a yanke hukuncin karshe kan ko za a kafa sabuwar jam’iyya ko a yi amfani da wata jam’iyyar kawai a ranar 30 ga Mayu.
A cewarsa:
“Kwamitin hadakar ya kafa kwamitoci biyu domin tantance yiwuwar yin rijistar sabuwar jam’iyya ko kuma shiga wata jam’iyya da ke da rijista.
“Kwamitin da ke duba yiwuwar shiga wata jam’iyya zai kasance karkashin Liyel Imoke, yayin da Rotimi Amaechi ke jagorantar kwamitin kafa sabuwar jam’iyya.”

Asali: Twitter
'El-Rufai ya gabatar da bukatar SDP' - Ardo
Umar Ardo ya kara da cewa har yanzu suna la’akari da ADC da SDP a matsayin jam'iyyun da za su iya zaɓar guda daya a ciki idan har kafa sabuwar jam’iyyar ba zai yiwu ba.
“Tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya gabatar da rahoto cewa SDP tana son a zabe ta a matsayin jam'iyyar hadaka. Don haka an sanya ranar 30 ga watan nan domin yanke hukunci, ko a bi ADC, SDP ko kuma a kafa sabuwar jam’iyya."
Ya kuma kara da cewa:
“Mun yanke shawarar tuntubar gwamnonin Arewa 19 domin tattauna wa da su kan matsalolin talauci, fatara, rashin tsaro da rashin ayyukan yi da ke addabar yankin Arewa.”
Hadakarsu Atiku ta amince da jam'iyyar SDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun amince da kafa hadakar siyasa domin tunkarar zaben 2027 tare da shiga jam’iyyar ADC.
Rahotanni sun bayyana cewa manyan ’yan siyasar uku sun gudanar da taro a Abuja, inda suka yanke shawarar amfani da ADC a matsayin jam'iyyar hadaka.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya ce PDP ba ta cancanta da zama jam’iyyar hadaka ba saboda matsalolinta sun yi tsanani matuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng