"Ba Zan Janye Wa Atiku ba," Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Kawo Cikas a Shirin 2027
- Prince Adewole Adebayo ya bayyana cewa ba zai janye wa Atiku Abubakar takara ba ko da kuwa ya shiga jam'iyyar SDP
- Adebayo, wanda ya yi takarar shugaban kasa a inuwar SDP a zaben 2023 ya ce yana girmama Atiku, amma ba zai iya janye masa ba
- Ya ce jam'iyyar SDP tana da ƙima da martaba kuma ƙofarta a buɗe take ga duk wanda ya amince da manufofinta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa ba zai janye ya bar wa Atiku Abubakar takara a 2027 ba.
Adewole Adebayo ya ce yana girmama tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, amma ba zai iya haƙura ya bar masa takara ba ko da sun haɗu a jam'iyya guda.

Asali: Twitter
Adebayo ya faɗi haka ne a wata hira da ya yi da Channels TV a shirin siyasa a yau ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ɗan siyasar ya yi tsokaci kan yunƙurin haɗaka tsakanin jam’iyyun adawa don kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa.
Adebayo ya ce ba zai janye wa Atiku ba
“Ba zan janye ba, kuma Atiku bai ce wani ya janye masa ba. Ni da Atiku ba za mu iya amfani da jam’iyyar SDP ba. SDP mallakin ‘yan Najeriya ne, ba wanda zai iya amfani da ita.
"Duk wanda ya aminta da SDP da manufofinta kuma yake ganin tana kan turba mai kyau, zai iya shigowa ya haɗa kai da mu. Amma duk wanda ke tunanin zai zo ne don amfani da jam’iyyar kawai, hakan ba zai yiwu ba.
“SDP ba jam’iyya ce da za a iya amfani da ita ba. Abin da za ka iya yi shi ne ka haɗa kai da jam’iyyar tare da girmama manufofinta da aikin da waɗanda ke cikinta suka riga suka yi."
- In ji Adewole Adebayo.

Asali: Twitter
Tsohon ɗan takarar SDP na shirin shiga haɗaka?
Dangane da Atiku, Adebayo ya nuna girmamawarsa amma ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai taba tuntubarsa kai tsaye ba kan batun haɗaka ba.
"Ina girmama Atiku, amma mutane ne ke magana a madadinsa. Ya san abin da yake yi, kuma yana da damar tuntubar mu kai tsaye. Idan yana son ya shiga SDP, zai zo ya fada mana da kansa," in ji shi.
Adebayo ya ce jam’iyyar SDP za ta tsaya kai da fata wajen kare mutuncinta da tsare gaskiya a siyasa, ba tare da barin wani ɗan siyasa ya mamaye ta ba inji rahoton Vanguard.
Hadakar Atiku Abubakar ta zaɓi jam'iyya?
A wani labarin, muna kawo rahoton cewa haɗakar da Atiku ke jagoranta ta musanta rahoton amincewa da ADC a matsayin jam'aiyyar da za ta yi amfani da ita.
Ta bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da rahoton wanda ya karaɗe kafafen watsa labarai, tana mai cewa karya ce mara tushe.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da manyan ƴan adawa karkashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa suka kudiri aniyar kawo ƙarshen mulkin APC a 2027.
Asali: Legit.ng