Wasu Manya daga Arewacin Najeriya Sun Cimma Matsaya kan Wanda Za Su Zaɓa a 2027
- Wasu manyan Arewa daga jihohi 19 da birnin Abuja sun ayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Sun bayyana cewa abubuwan alherin da Shugaba Tinubu ya yi a shekaru biyu kaɗai sun cancanci a sake ba shi dama karo na biyu a 2027
- A cewarsu, Bola Tinubu ya kawo sauyi a fannonin tsaro, tattalin arziki, sannan ya tabbatar da ƴancin kananan hukumomin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jagororin al'umma daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja karkashin kungiyar Northern Bridge Builders Forum, sun yanke wanda za su zaɓa a 2027.
Manyan Arewan sun ayyana shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda za su marawa baya ya zarce zango na biyu a gadon mulkin Najeriya.

Asali: Twitter
Shugaban kungiyar kuma tsohon sanata, Joel Danlami Ikenya ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Tinubu ya samu goyon bayan manyan Arewa
Ya ce sun cimma wannan matsaya ne biyo bayan “kyakkyawan aiki” da Tinubu ke yi a fadin kasar nan a cikin shekaru biyun da suka gabata.
Sanata Ikenya ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo sauye-sauye a fannonin tsaro, farfaɗo da tattalin arziki, ƴancin kananan hukumomi, da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da haɗin kan kasa.
Ya ce:
“A ƙarƙashin wannan gwamnati, Najeriya na shaida muhimman sauye-sauye da ci gaba, musamman a fannin tsaro da kuma ƴancin kananan hukumomi,” in ji Ikenya.
Mayan Arewa sun aika saƙo ga Tinubu
Duk da haka, ya ja hankalin shugaban ƙasa da ya ƙara zage dantse wajen magance ayyukan ‘yan ta’adda, Boko Haram, ISWAP, da sauran kungiyoyin ta’addanci a wasu sassan Arewacin Najeriya.
“Muna kira da a ci gaba da ɗaukar matakai masu karfi don dakile wadannan miyagun ayyuka da suka sake dabaibaye yankuna da dama," in ji shi.
Ikenya ya kuma bukaci majalisar dokokin ƙasa da ta hanzarta amincewa da kudurin kafa dakarun gadin jeji, domin su kasance kariya a dazuka da ke zama mafakar ‘yan ta’adda.

Asali: Twitter
An buƙaci Tinubu ya waiwayi manoma
A rahoton The Nation, Sanata Ikenya ya ci gaba da cewa:
"Haka kuma muna kira da a samar da kayayyakin aikin gona ga manoma cikin lokaci domin su samu damar yin noman da ya dace a kan lokaci."
A cewarsa, dole ne a nuna hakuri da goyon baya ga manufofin shugaban kasa, domin ana gina kasar ne ba kawai don yanzu ba, har ma da ‘yan baya.
“Dole ne mu guji shiga tarkon wasu da ke son rushe nasarorin da ake kokarin cimmawa saboda son rai,” in ji shi.
A karshe, kungiyar jagororin Arewa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Tinubu domin ya ci gaba da mulki a wa’adi na biyu na shekarar 2027.
2027: APC a Arewa ta Tsakiya ta bi sahu
A wani rahoton, kun ji cewa masu ruwa da tsakin APC a Arewa ta Tsakiya sun tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Shugabannin APC a yankin wanda suka gaɗa da gwamnoni, ƴan Majalisa da sauran jiga-jigai sun cimma wannan matsa ne a taron da suka yi a Abuja.
A yayin taron, mahalarta sun kuma kada kuri’ar yarda da shugabancin Tinubu, suka ce ya kawo sauye-sauye masu ma’ana musamman a yankinsu.
Asali: Legit.ng