2027: ADC Za Ta Yi Taro kan Maganar Kulla Kawance da Atiku, Obi da El Rufa'i
- ADC za ta gudanar da muhimmin taro a Abuja domin karɓar rahoton kwamitocin tattaunawa da suka shiga shirin haɗa kawance da manyan ’yan adawa
- Rahotanni sun nuna manyan ’yan siyasa da suka haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi sun zaɓi ADC a matsayin dandalin tsayawa takara
- Shugaban ADC ya ce ƙasar na buƙatar ceto, kuma sun kwashe fiye da wata shida suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban kan maganar hadakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC za ta gudanar da taron gaggawa a yau Alhamis a Abuja domin karɓar rahoton kwamitoci biyu da suka wakilce ta a tattaunawa da wasu fitattun ’yan siyasa na adawa.
Wannan na zuwa ne bayan da aka bayyana cewa wasu fitattun ’yan adawa daga jam’iyyun siyasa daban-daban sun zaɓi ADC a matsayin jam’iyyar hadaka.

Asali: Facebook
Tribune ta wallafa cewa ana sa ran ADC za ta jagoranci ƙawancen da 'yan adawa za su yi domin fitar da ɗan takara da zai fuskanci Shugaba Bola Tinubu a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Fitattun ’yan adawa sun amince da ADC
Arise News ta wallafa cewa ’yan adawa da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023 Peter Obi na cikin maganar hadakar.
Haka zalika an ce tsofaffin gwamnoni Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi ne suka amince da amfani da ADC a matsayin dandalin kawance.

Asali: UGC
Hakan ya biyo bayan wani taro da suka yi a Abuja a daren Talata, inda suka yanke shawarar cewa ADC ce ke da tsarin da yafi dacewa da burinsu na tsayawa takara a siyasar 2027.
A halin yanzu, ana sa ran kwamitocin da ADC ta kafa za su gabatar da cikakken rahoto a gaban shugabannin jam’iyyar a yau, wanda hakan zai sa a amince da sabbin dabarun siyasa.
ADC ta shafe wata 6 tana tattaunawa
A cewar shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Ralph Okey Nwosu, kwamitoci biyu ne suka wakilci jam’iyyar.
Nwosu ya ce ɗaya kwamitin na karkashin mataimakin shugaban jam’iyya Dr Bamidele Ganiyu Ajadi, ɗaya kuma karkashin shugaban kwamitin amintattu Dr Mani Ibrahim Aman.
Ya ce kwamitocin sun yi tattaki zuwa sassa daban-daban na ƙasar, suna tattaunawa da sanannun ’yan siyasa, kungiyoyin farar hula da kuma ’yan ƙasa domin kafa sabuwar tafiya.
Nwosu ya ƙara da cewa ba zai iya fitar da cikakken bayani ba tukuna har sai bayan taron yau, inda za a bayyana dukkan matakan da aka ɗauka don tafiyar da shirin kawancen.
Umahi ya nemi Obi ya yi watsi da hadaka
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka na kasa, Dave Umahi ya yi kira ga Peter Obi ya yi watsi da maganar hadaka a 2027.
Dave Umahi ya ce ya fi dacewa ga Peter Obi ya hada kai da gwamnatin shugaba Bola Tinubu maimakon yin takara.
Ministan ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ayyuka sosai wa mutanen Peter Obi a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng