Gwamnan Oyo Ya Fadi Matsayarsa kan Rabuwa da PDP zuwa Wata Jam'iyya

Gwamnan Oyo Ya Fadi Matsayarsa kan Rabuwa da PDP zuwa Wata Jam'iyya

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce ba zai bar PDP ba, duk da sauyin sheka da rikice-rikicen cikin gida da ake fuskanta a jam’iyyar
  • Ya bayyana cewa ikirarin da wasu ke yi na cewa akwai rikicin gida da zai hana PDP tasiri, bai hana ta samun nasara a zaben Oyo ba
  • Seyi Makinde ya nanata cewa jam'iyyar na da karfi, domin ta ci gaba da wanzuwa duk da cewa ta rasa mulkin Najeriya tun zaben 2015

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo – Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sake jaddada cewa ba shi da niyyar barin jam’iyyar PDP duk da sauyin sheka da kuma matsalolin cikin gida da ake fama da su a yanzu.

Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin bikin rantsar da sababbin shugabannin PDP na yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Ibadan.

Makinde
Gwamnan Oyo ya ce yana nan daram a PDP Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Gwamna Makinde ya bayyana cewa PDP za ta ci gaba da kasancewa tare da talakawa da muradunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Kalamansa na zuwa ne a lokacin da ake jita-jitar cewa wasu gwamnoni na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan Oyo ya magantu kan komawa APC

The Guardian ta ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde ya ce akwai tambayoyi da ake yi dangane da wasu shugabannin PDP da ke shirin barin PDP zuwa wata jam’iyya.

Ya ce:

“Mutane na tambayar mu a matsayin shugabanni na jam’iyyar cewa ana ta sauyin sheka, har da gwamnoni, wasu kuma na barazanar sauya sheka. Suna tambaya kan makomar PDP."
“Na gaya wa mutane cewa ba za mu damu ba, saboda masu yunwa ne yunwa ke ta sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Ya bayyana yakinin cewa duk lokacin da APC ta fada yunwa, wadannan yan siyasa da ke rububinta a yanzu za su ba da labari.

‘Zan ci gaba da zama a PDP,’ Makinde

Gwamnan Oyo ya tabbatar wa da magoya bayan jam’iyyar cewa PDP na nan daram duk da matsalolin sauyin sheka da ake fuskanta.

Makinde
Gwamnan Oyo ya ce har yanzu PDP da kwarinta Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamna Makinde ya ce:

“Na karanta wata tattaunawa da ta ce PDP tana gina shugabanni ne masu karfi amma ba ta da karfin jam'iyya. Amma ni ban yarda da hakan ba."
“PDP ta rasa mulki a matakin tarayya tun 2015 amma hakan bai kashe jam’iyyar ba. Daga baya ma na karanta wani rahoto a kusan shekarar 2017 wanda ya tabo rikice-rikicen PDP a jihar Oyo. Duk da wadannan rikice-rikice, PDP ta lashe zabe a jihar Oyo.”

Sharadin Sanatocin PDP na shiga hadakar Atiku

A baya, mun wallafa cewa Sanatocin jam’iyyar PDP a Majalisar Dattawa sun bayyana cewa ba su da matsala da shirin kafa haɗakar jam’iyyu domin fuskantar APC a babban zaben 2027.

Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro daga Binuwai ta Kudu, ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da sanatocin suka yi a birnin Abuja ranar Talata.

Ya kara da bayyana cewa a matsayin PDP na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, tana da cikakken karfin da zai iya karɓar duk masu kishin kafa irin wannan haɗaka don samar da sauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »