Kano: APC Ta Fadi Dalilin Adawa da Sauya Shekar Rabi'u Musa Kwankwaso
- APC ta jaddada matsayinta na kin amincewa da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa jam'iyya saboda wasu daga cikin halayensa
- Sakataren yada labaran jam'iyyar a Kano, Ahmed S. Aruwa ne ya bayyana haka a tattaunarsa da Legit kan adawa da shigar Kwankwaso APC
- Ahmed S. Aruwa ya zargi Kwankwaso da kin bin jagoranci kuma yana haddasa rikice-rikice a duk inda ya shiga jam'iyya idan ba a bi shi ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana dalilin da ya sanya take adawa da duk wan yunkuri na dawowar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cikinta.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar reshen jihar, Ahmed S. Aruwa, ne ya bayyana dalilinsu a hirarsa da Legit kan yadda suke adawa da rade-radin cewa Kwankwasi na ƙoƙarin komawa APC.

Asali: Facebook
Wasu jiga-jigan APC irinsu karamin Ministan gidaje, Yusuf Ata sun sha nanata cewa jam’iyyar ba ta da buƙatar Rabi’u Musa Kwankwaso kafin ta lashe zaɓe, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
APC: "Kwankwaso bai bin na gaba da shi"
A hirarsa da Legit, Ahmed S. Aruwa ya ce Sanata Rabi’u Kwankwaso ba ya bin tsarin jagoranci, sannan ya kan tayar da husuma a duk inda ya shiga, musamman idan ba a bi umarninsa ba.
A cewarsa:
"Ba mu na ƙin Rabi’u Musa Kwankwaso ba ne, muna ƙin rigimarsa ne. Mutum ne wanda kullum, idan kuna siyasa da shi, sai dai ya mallake kowa da komai, kuma ba wanda ya isa ya yi magana ko ya nuna buƙatarsa."
"Ko lokacin da suka kafa gwamnatin Kano, har ma da nadin kansiloli da sauran abubuwa da dama, sai a ce sai an jira madugu ya zo."
Ya ƙara da cewa APC jam’iyya ce ta kowa da kowa, kuma babu wanda ya yi shawara da Kwankwaso kafin ya aminta da tafiyar Bola Tinubu.
APC ta fadi matsayinta kan tafiya da Kwankwaso
Ahmed S. Aruwa ya ce za su iya yin siyasa da duk wanda zai amfanar da jam’iyyar, har da Sanata Kwankwaso, muddin ba zai shigo da halayensa na ƙoƙarin mallake kowa ba.
Ya ƙara da cewa shigowar Kwankwaso cikin APC zai iya haifar da babban nakasu ga ƙoƙarin da suke yi na samun kuri’u ga Bola Tinubu a jihar Kano, musamman idan ya tsaya takara a 2027.

Asali: Facebook
Ahmed S Aruwa ya ce:
"Rabi’u Musa Kwankwaso idan ya shigo, ba ka da iko, ba ka isa ka yi magana ba. Kuma suna da gwamnati a jihar Kano; duk wani abu da za a yi, sai a ce gwamnati ce. Daga ƙarshe, abin da ya ga dama shi za su yi.
"Sai a ƙarshe a shiga siyasar cikin gida da rikice-rikice, maimakon mu nemowa Tinubu abin da yake nema — ko da 25% na ƙuri’u ne — sai wata jam’iyya ta yi amfani da rigimar ta dauke wannan 25% ɗin."
Ya ce irin wannan hali na Sanata Kwankwaso ne ya sa tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyya a lokuta daban-daban.
Sai dai a baya an ji Ibrahim Shekarau ya nuna babu laifin Kwankwaso a sabanin da suka rika samu da shi a jam'iyyun APC, PDP da kuma NNPP.
Ahmed S Aruwa ya kara da cewa duk magoya bayan Tinubu da ke ganin ana bukatar Kwankwaso a APC sun tafka kuskure, kuma za su gane kurensu idan suka jawo zuwa cikinsu.
NNPP: 'Babu rikici da Kwankwaso'
A baya, mun wallafa cewa mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya karyata rahoton cewa akwai rikici a cikin jam’iyyar kamar yadda ake ta yaɗawa a wasu bangarori.
Johnson ya ce sauya sheƙa da sabani tsakanin ɓangarori ba sababbin abubuwa ba ne a siyasar Najeriya, musamman idan jam’iyya ta fara samun karɓuwa a tsakanin talakawan kasa.
Ya ce NNPP na ƙara samun karɓuwa, musamman daga matasa da suka amfana da shirin tallafi na karatu da Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf suka ƙaddamar a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng