2027: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Samun Goyon Baya daga Arewa, Ƴan Majalisa 12 Sun Bi Sahu
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da samun goyon baya yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027
- Sanatoci biyu da ƴan Majalisar Wakilai 10 na APC daga jihar Benuwai sun ayyana goyon bayansu ga Shugaba Tinubu domin ya zarce
- Sun kuma buƙaci gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Mambobin Majalisar Tarayya da suka fito daga jihar Benuwai a Arewa ta Tsakiya ƙarƙashin inuwar APC sun ayyana goyon bayansu ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ƴan Majalisar da suka haɗa da sanatoci da mambobin majalisar wakilai sun amince Shugaba Tinubu ya nemi zango na biyu a babban zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa ƴan Majalisar sun sanar da matsayarsu a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Bayan haka, sun bukaci gwamnan Benue, Rabaran Hyacinth Alia, da ya hada kai da gwamnatin tarayya domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi al'umma a jihar.
Bola Tinubu na ƙara samun goyon baya
Wannan dai na zuwa ne bayan masu ruwa da tsakin APC a shiyyar Arewa maso Yamma sun jaddada goyon bsyansu ga tazarcem Shugaba Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Jiga-jigan yankin ciki har da shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje sun cimma wannan matsaya ne a taron da suka yi a jihar Kaduna.
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon. Tajudeen Abbas ne ya gabatar da kudirin goyon bayan Tinubu karo na biyu kuma gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris ya mara masa baya.
Daga nan suka kaɗa ƙuri'ar marawa shugaban kasa, Bola Tinubu baya domin ya zarce zango na biyu a 2027.
Ƴan Majalisar Tarayya 12 sun bi sahunsu
A yau Laraba, ƴan Majalisar tarayya daga Benuwai sun bi sahu, sun ce suna tarw da Bola Ahmed Tinubu a zaɓe na gaba.
Wadanda suka mara wa Tinubu baya sun hada da Sanatoci biyu da ’yan majalisar wakilai 12 duk daga jihar Benue.

Asali: Facebook
Sanatocin biyu da suka bayyana goyon bayansu sune Sanata Titus Zam (Benuwai ta Arewa maso Yamma) da Sanata Emmanuel Udende (Benuwai ta Arewa maso Gabas).
’Yan majalisar wakilai 10 sun hada da:
1. Hon. Dickson Tarkigir
2. Hon. David Ogewu
3. Hon. Sesoo Ikpagher
4. Hon. Terseer Ugbor
5. Hon. Asema Achado
6. Hon. Philip Agbese
7. Hon. Sekav Iyoryom
8. Hon. Regina Akume
9. Hon. Blessing Onuh
10. Hon. Solomon Wombo.
Yadda ƴan Arewa za su yi alkalanci a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya yi tsokaci kan goyon bayan ƴan APC a Arewa maso Yamma suka yi wa Bola Tinubu.
Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ba haka nan ƴan yankin za su sake zaɓen Tinubu, gwamnoni da sauran shugabannin siyasa ba.
Ya ce mutanen yankin Arewa maso Yamma za su yi wa 'yan siyasa alkalanci bisa wahalhalun da suka sha na tashin hankali, kashe-kashe da talauci a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng