2027: Ana Neman Peter Obi Ya Yi Watsi da Hadaka da Atiku, Ya Shiga Tafiyar Tinubu
- Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya nemi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, da ya haɗa kai da gwamnonin Kudu maso Gabas a marawa Bola Tinubu baya
- Dave Umahi ya ce yankin Kudu maso Gabas na amfana da manyan ayyuka da kulawa daga gwamnatin Bola Tinubu fiye da yadda aka saba a baya
- Ministan ya kuma bayyana cewa kashi 80 na sashen farko na hanyar Lagos-Calabar ya kammala, kuma za a fara karɓar kuɗin haraji a hanyar a Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bukaci tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi ya goyi bayan Bola Tinubu.
Ministan ya ce ya kamata Obi ya haɗa kai da sauran shugabannin Kudu maso Gabas wajen marawa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya.

Asali: Facebook
Rahoton Channels TV ya nuna cewa Umahi ya fadi haka ne a wata hira da ya yi a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A cewarsa, shugabannin Kudu maso Gabas suna goyon bayan shugaba Tinubu duk da bambancin jam’iyyu, kasancewar ana samun sauyi da ci gaba a yankin karkashin gwamnatinsa.
Umahi ya nemi Peter Obi ya marawa Tinubu baya
Ministan ya ce ba domin bukatun kai ake neman shugabanci ba, sai dai domin al’umma, don haka akwai buƙatar Obi ya goyi bayan Tinubu.
Umahi ya bayyana haka ne domin a cewarsa Peter Obi ya ga Tinubu ya soma aiwatar da ayyukan da shi ma zai so yi wa mutanensa.
Vanguard ta wallafa cewa Dave Umahi ya ce:
“Ina roƙon ɗan’uwana, mai girma Peter Obi, da ya haɗa kai da mu wajen yin aiki da shugaba Tinubu.
"Dole ne ya kasance cikin wannan tafiya da za mu mara wa shugaban ƙasa baya a 2027,”
Umahi ya fadi ayyukan Tinubu a yankin Obi
Umahi ya bayyana cewa ana samun manyan ayyuka a yankin Kudu maso Gabas, musamman hanyar Lagos-Calabar wadda kashi 80% na sashen farko ya kusa ƙarewa.
Ya ce za a fara karɓar kuɗin haraji a Disamba, kuma ana sa ran mayar da kudin da aka kashe cikin shekara 10.

Asali: Getty Images
Umahi: 'Kudu maso gabas na jin dadin Tinubu'
Umahi ya jaddada cewa zamanin da Kudu maso Gabas ke kukan rashin kulawar tarayya ya wuce, domin yanzu ana aiwatar da manyan ayyuka a yankin.
Ya ce hakan na nuna adalci da jajircewar shugaban ƙasa wajen tabbatar da aikin yi da ci gaba a kowane yanki.
Obi da Atiku sun yi magana kan hadaka a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun musanta cimma matsaya kan hadaka.
Atiku Abubakar ya ce ana tattauna yadda za a kawo sauyi a Najeriya da kawar da APC amma ba a iso maganar raba kujerun takara ba.
Haka zalika shi ma Peter Obi ya ce ba tsayawa takara ba ce babbar damuwarsa a yanzu, burinsa shi ne kawo sauyi a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng