Rikicin Kwankwasiyya Ya Budewa Barau Kofar Karbar 'Yan NNPP zuwa APC a Kano
- Sanata Barau Jibrin ya karɓi sababbin mambobi a APC daga ƙananan hukumomin Kano ta Arewa, ciki har da shugabannin siyasa biyu daga jam’iyyar NNPP
- Hon. Abubakar Ibrahim Makwa da Hon. Jamilu Salisu Bros sun jagoranci ɗaruruwan magoya bayansu a Kabo zuwa APC kan rikice-rikicen Kwankwasiyya
- Kafin hakan, Barau ya halarci zaman majalisar ECOWAS a Abuja, inda ya gode wa Bola Tinubu bisa jagoranci da hangen nesa kan haɗin kan Afrika ta Yamma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta samu ƙarin ƙarfi a yankin Kano ta Arewa bayan da fitattun ‘yan siyasa biyu daga NNPP suka jagoranci ɗaruruwan magoya bayansu suka sauya sheka.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karɓi sababbin mambobin a wani taron siyasa da aka gudanar a Abuja.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sauya sheƙar na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Barau ya bayyana goyon bayansa ga ci gaban dimokiraɗiyya da haɗin kan ƙasa a majalisar ECOWAS.
'Yan NNPP sun koma APC kan rikicin Kwankwasiyya
Ɗaya daga cikin rukunan da suka sauya sheƙa daga NNPP sun kasance karkashin jagorancin tsohon ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Kabo, Hon. Abubakar Ibrahim Makwa.
Rukuni na biyu kuma sun kasance karkashin tsohon ɗan takarar kansila a gundumar Kabo, kuma shugaban ‘yan takarar kansiloli daga Kano ta Arewa, Hon. Jamilu Salisu Bros.
Dukkan su sun bayyana cewa sun fice daga NNPP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da rashin daidaito da ke addabar Kwankwasiyya.
Sun ce jam’iyyar NNPP ba ta da kyakkyawar makoma, musamman ga matasa da ke fatan samun wakilci da ci gaba.
Barau ya ce jam'iyyar APC gida ce ga kowa
Yayin da yake karɓar sabbin mambobin, Sanata Barau Jibrin ya bayyana farin cikinsa da hakan, yana mai cewa APC jam’iyya ce da ke da cikakken tsari da manufofi na ciyar da al’umma gaba.
Ya tabbatar musu da cewa za su sami dama da wakilci a sabuwar tafiyar da suka fara, kuma gwamnatin Bola Tinubu za ta ci gaba da tallafawa ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.

Asali: Facebook
Kafin taron sauya sheƙar, Sanata Barau ya halarci zaman farko na majalisar ECOWAS da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 21 ga Mayu 2025 bayan dawowa daga hutu.
NNPP ta ce APC na mata bita da kulli
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta ce APC ce ke mata bita da kulli a kan rikicin da ake gani kamar yana faruwa a cikinta.
Mai magana da yawun NNPP na kasa ya ce tsagin da suka balle daga jam'iyyar suna nuna goyon baya ga APC karara duk da suna cewa suna adawa.
Kakakin jam'iyyar, Ladipo Johnson ya bayyana cewa jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai cigaba da zama a NNPP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng