'Yadda Marigayi Abba Kyari Ya ba Mu Cin Hanci ni da Rimi': Sule Lamido Ya Yi Bankaɗa

'Yadda Marigayi Abba Kyari Ya ba Mu Cin Hanci ni da Rimi': Sule Lamido Ya Yi Bankaɗa

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce shi da marigayi Alhaji Abubakar Rimi sun taba ki karɓar N160m na cin hanci
  • Lamido ya marigayi Abba Kyari ne ya kawo kudin a matsayin cin hanci domin samun damar zama mataimakin Olusegun Obasanjo
  • Tsohon gwamnan ya bayyana hakan a cikin littafinsa, yana cewa sun fusata da bukatarsa inda suka kori Kyari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi wata bankaɗa kan marigayi Abba Kyari.

Lamido ya ce shi da marigayi Abubakar Rimi sun ƙi karɓar cin hancin N160m daga Kyari domin samun goyon bayan su wajen zama mataimakin Olusegun Obasanjo.

Sule Lamido ya kunyata Abba Kyari
Sule Lamido ya fadi yadda suka ki karbar cin hanci daga Abba Kyari. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Facebook

Sule Lamido ya yi magana kan Abba Kyari

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wani bangare na littafinsa mai suna 'Being True to Myself', cewar Punch

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Lamido ya kaddamar da littafin ne a ranar 13 ga Mayun 2025 da muke ciki a birnin Tarayya, Abuja.

Tsohon ministan ya ce waɗanda ake tunanin ba su mukamin sun haɗa da Jibril Aminu, Adamu Ciroma, da Abubakar Rimi.

Sule Lamido ya ce Kyari, wanda daga baya ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa a zamanin Muhammadu Buhari, ya zo da takardar banki ta N160m.

A babi na tara, 'Abdulsalami’s Transition and Formation of the PDP', Lamido ya ce Kyari ya bar wajen cikin kunya bayan sun ƙi karɓar kuɗin da ya kawo musu.

Ya ce:

“Matashin ya gaishe ni da ‘Ranka ya daɗe, Sule!’ Sannan ya nuna abokinsa ya miƙo hannu yana cewa ‘Wannan Abba Kyari ne.
"Ya kawo takardar banki na N160m don taimakawa jam’iyya wajen kamfe.’”
“Rimi da ni muka rude, mun kasa gaskata abin da muka ji, muka kalli mutanen biyu, suma suna kallon mu da murmushi ba kunya.”

Lamido ya magantu kan marigayi Abba Kyari
Sule Lamido ya ce sun ki karbar cin hanci daga Abba Kyari tun yana raye. Hoto: Sule Lamido.
Asali: Twitter

Yadda Lamido ya fusata da marigayi Abba Kyari

Lamido ya bayyana yadda suka fusata, idanunsa suka yi jawur duba da kokarin sayan su da marigayi Abba Kyari ya yi.

Ya kara da cewa:

“Na ce, ‘Me? Don Allah, kun kawo mana kuɗi don siyan mu? Ku na bani N160m saboda Kyari da ba mu san shi ba ya zama mataimaki?’”
“Idanuwana suka yi ja cikin fushi, na ce, ‘Ba ku da hankali ko? Wawa kawai!’ Suka tafi cikin kunya, ba tare da sun ce komai ba.”
“Matashin ya kawo Kyari domin yana ganin mu ni da Rimi mu ne ke da mahimmanci wajen zaben wanda zai zama mataimakin shugaban ƙasa.”

Amaechi ya fadi dalilin rigimarsa da Lamido

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa shi da Sule Lamido sun yi abota mai karfi lokacin da suke gwamnoni.

Amaechi ya ce sun rabu ne bayan Sule ya yanke shawarar shiga jam’iyyar SDP, maimakon su zauna a APC kamar yadda suka amince.

Tsohon ministan ya ce ya dauka tsohon ministan harkokin wajen yana da ra’ayin sauyi kamar shi, amma daga baya ya fahimci bambanci a siyasarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »