2027: NNPP Ta Ce Kwankwaso zai fi Yi wa Tinubu Amfani a kan Ganduje

2027: NNPP Ta Ce Kwankwaso zai fi Yi wa Tinubu Amfani a kan Ganduje

  • Ladipo Johnson ya musanta cewa rikici ne ke addabar jam’iyyar NNPP, yana mai cewa sauya sheka da ƙirƙirar bangarori ba sababbin abubuwa ba ne a siyasa
  • Kakakin tsagin NNPP ya ce harin siyasa da ake kai wa jam’iyyar wani ɓangare ne na ƙoƙarin lalata mata tafiya, musamman daga wasu ‘yan jam’iyyar APC
  • Johnson ya jaddada cewa Rabiu Kwankwaso bai yanke shawarar sauya sheka ko raba kai da jam’iyyar ba, kuma NNPP na da tasiri sosai a matakin ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai magana da yawun tsagin NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya ce jam’iyyar ba ta cikin rikici kamar yadda ake yayatawa, duk da ficewar wasu ‘yan majalisa daga cikinta.

A cewar Johnson, NNPP na ci gaba da kara ƙarfi a ƙasa, musamman daga matasa da suka amfana da shirye-shiryen tallafin karatu na Rabiu Kwankwaso da kuma Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso
Kakakin tsagin NNPP ya ce APC na musu bita da kulli. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso|Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da Arise News, inda ya ce sauya sheka da rikicin ɓangare ba sababbin abubuwa ba ne a siyasar Najeriya, musamman idan jam’iyya ta fara samun karɓuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Johnson: 'NNPP ba ta damu da sauya sheka ba'

Johnson ya bayyana cewa ficewar Sanata Ka’u Ismaila da wasu ‘yan majalisa ba wata matsala ba ce da za ta girgiza NNPP, yana mai cewa hakan na daga cikin halayen 'yan siyasar Najeriya.

Ya ƙara da cewa babu wani mataki da Sanata Kwankwaso ko jam’iyyar ta yanke dangane da komawa APC ko wata jam’iyya,

Johnson ya ce ana son lalata jam'iyyar NNPP

Johnson ya ce wasu daga cikin waɗanda aka kora daga jam’iyyar na amfani da tsohon tambari da tsarin jam’iyyar da aka canza tun watan Afrilu 2024 don yaudara.

Ya zargi wasu kamar Dr Aniebonam da Olakosi da yin aiki da APC don tayar da ƙura a cikin NNPP, yana mai cewa:

“A kowane rikici da aka yi a Kano — zuwa kotu, batun sarauta, da zaɓen ƙananan hukumomi — suna goyon bayan APC.”
Kwankwaso
NNPP ta ce Kwankwaso na da tasiri a Najeriya. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

'Kwankwaso zai fi Ganduje amfani' - Kakakin NNPP

Johnson ya ce Kwankwasiyya da NNPP na samun ƙarin matasa da suka amfana da guraben karatu da sauran shiryen tallafi.

Game da ko Kwankwaso zai sake komawa APC, Johnson ya ce:

“Kwankwaso ba mutum ba ne da ke yanke shawara saboda son rai. Duk lokacin da ya sauya sheka, yana da dalilai.”

Da aka tambaye shi ko Kwankwaso zai iya shiga APC karkashin Abdullahi Ganduje, Johson ya bayyana cewa Kwankwaso mutum ne mai tasiri a siyasar Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa Kwankwaso zai fi yi wa Bola Tinubu amfani a siyasa a kan Abdullahi Ganduje, kuma kowa ma ya san da hakan.

'Yan Kwankwasiyya sun gargadi Abba Kabir

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ta ba gargadi Abba Kabir Yusuf kan alaka da 'yan-ba-ni-na-iya.

Kungiyar ta ce akwai wadanda suke rike da mukamai amma burinsu shi ne tara abin duniya ba kawo cigaba ba.

Shugaban kungiyar ya bukaci Abba Kabir Yusuf ya mayar da hankali kan tafiya da 'yan Kwankwasiyya da suka sha wahala a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »