Atiku da Obi Sun Yi Zance Iri Daya wajen Musanya Cimma Maganar Hadaka a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi sun nesanta kansu daga jita-jitar sun kulla yarjejeniyar raba mukamai a 2027
- Peter Obi ya ce ba zai zama mataimakin kowa ba, yana mai cewa jita-jitar wata hanya ce ta siyasar son kai da ke bata hadin kai a Najeriya
- Kungiyar Obidient Movement da ke goyon bayan Obi ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, tana cewa babu wata matsaya da aka cimma har yanzu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsofaffin 'yan takarar shugaban ƙasa a 2023 na jam’iyyun PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi, sun musanta wani rahoto da ke cewa sun cimma yarjejeniyar hadaka a 2027.
Rahoton da ya janyo ce-ce-ku-ce ya bayyana cewa Atiku ya miƙa wa Obi tayin kujerar mataimaki a zaɓen mai zuwa, tare da alkawarin tsayawa wa’adi guda kacal.

Asali: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa an ce an fara tattaunawa kan wannan lamari ne a wani taro da suka yi a ƙasar Birtaniya a farkon shekarar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Obi ya nesanta kansa daga wannan batu, yana mai cewa ba zai zama mataimakin kowa ba, kuma manufarsa ita ce kyautata shugabanci da warware matsalolin da ke damun ‘yan Najeriya.
Atiku ya karyata cewa zai dauki Obi mataimaki
Atiku Abubakar, ta bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya ce batun cewa an cimma matsaya jita-jita ce kawai.
Ya ce duk wata tattaunawa da ake yi tsakanin manyan ‘yan adawa kamar Obi da Atiku na nufin samar da wata sabuwar kafa mai ƙarfi domin ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Paul Ibe ya ce:
“Idan har ana magana kan raba kujeru tun yanzu, to hakan ya saba da tsarin da ake bi.
"Tattaunawa dai na gudana, kuma burinmu shi ne kafa wata hadaka mai ma’ana da zai amfanar da talaka.”
Punch ta wallafa cewa shi ma Peter Obi ya musanta cewa ya tattauna wani batu na zama mataimakin Atiku.
Obi ya ce:
“Ba siyasa nake domin neman kujera ba. Na dawo daga Rome yanzu, kuma burina shi ne inganta ilimin ‘ya’yanmu da rage talauci da rashin lafiya. Wannan ce siyasa mai ma’ana.”
Martanin magoya bayan Obi kan hadaka
Kungiyar magoya bayan Peter Obi, wato Obidient Movement, ta bayyana cewa ba a cimma yanke hukunci dangane da tsayawa takara tare da Atiku ba.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Yunusa Tanko, ya ce:
“Na yi magana da Obi kai tsaye, kuma babu wani abu makamancin haka da aka tattauna. Wadannan jita-jita na cutar da yunkurin kafa hadaka.”
A cewar Daraktar Hulda da Jama’a ta ƙungiyar, Hajiya Nana Kazaure sun fuskanci tambayoyi masu yawa daga mambobi a gida da waje dangane da batun.

Asali: Facebook
Ra'ayoyin masana kan hadakar Atiku da Obi
Farfesa Gbade Ojo ya bayyana cewa kafa hadaka tsakanin Atiku da Obi na ɗauke da hadari a harkar siyasa. A cewarsa, wasu na ganin lokaci ya yi da Atiku zai janye daga siyasa gaba ɗaya.
Shi ma Dr Ibrahim Yahaya daga Jami’ar Al-Hikmah ya ce kalaman Obi a baya-bayan nan, musamman bayan dawowarsa daga Rome, na iya rusa duk wani fatan kafa hadaka tsakaninsu.
ADC za ta shiga hadaka a zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar ADC na kasa ya bayyana cewa a shirye suke wajen shiga hadakar 'yan adawa.
Shugaban ADC ya bayyana cewa nan gaba kadan zai bayyana matakan da suke dauka domin kawo karshen mulkin APC.
Legit ta rahoto cewa ADC ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin neman tara kuri'u sama da miliyan 30 domin kayar da Bola Tinubu a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng