NNPP Ta Nemi Gafarar Tinubu da Ganduje kan Zafafan Kalaman Kwankwaso

NNPP Ta Nemi Gafarar Tinubu da Ganduje kan Zafafan Kalaman Kwankwaso

  • Tsagin jam’iyyar NNPP ya nemi gafarar shugaba Bola Tinubu da APC kan wasu kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi
  • NNPP ta ce Kwankwaso ba ɗan jam’iyyar ba ne tun bayan sallamarsa tare da daina aiki da Kwankwasiyya da NNPP ta yi
  • Jam’iyyar ta bayyana cewa hukuncin kotu ya tabbatar da korar Kwankwaso daga NNPP, kuma ba ya wakiltarta a ko ina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsagin jam’iyyar NNPP ya bayyana damuwa tare da neman afuwa daga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC kan wasu kalaman da Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi.

Tsagin jam'iyyar ya ce akwai cin fuska cikin kalaman da tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kwanan nan.

Kwankwaso
NNPP ta ba Tinubu hakuri kan kalaman Kwakwaso. Hoto: Bayo Onanuga|Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa tsagin NNPP ya ce Sanata Kwankwaso ya riga ya fita daga cikinta tun tuni, don haka bai da hurumin amfani da sunanta wajen sukar shugabanci ko jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsagin NNPP na ƙasa, Dr Oginni Olaposi, ya fitar a Legas ranar Lahadi.

Tsagin NNPP ya nesanta kansa da Kwankwaso

Oginni Olaposi ya bayyana cewa NNPP ta sallami Kwankwaso da Kwankwasiyya, inda ya ce duk wani abu da ya fito daga gare su, ra’ayinsu ne na kashin kai ba matsayar jam’iyyar ba.

Vanguard ta wallafa cewa Olaposi ya ce:

“Muna neman gafarar Shugaba Tinubu da dukkan 'yan APC, musamman jagoranta, Dr Abdullahi Ganduje, kan cian fuska da suka fuskanta daga Kwankwaso.”

Olposi ya jaddada cewa Kwankwaso bai da hurumin magana da sunan NNPP, kuma bai kamata ya rika sukar gwamnati da jam’iyya mai mulki da sunan NNPP ba.

Tsagin NNPP ya ce kotu ta kori Kwankwaso

Mai magana da yawun jam’iyyar ya bayyana cewa kotuna da dama, ciki har da ta Abuja da Abia sun tabbatar da hukuncin sallamar Kwankwaso daga NNPP.

Ya ce:

“Ya kamata Kwankwaso ya tsaya a matsayinsa, ya daina sukar wasu saboda magoya bayansa suna komawa APC.”

Jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin, Dr Boniface Aniebonam ta ce ba ta amince da cin fuska da sunan siyasa ba.

Olaposi ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da jama’a da su daina danganta Kwankwaso da NNPP, domin kuwa a yanzu shi ba kowa ba ne face shugaban tafiyar Kwankwasiyya kawai.

Ya ƙare da cewa NNPP na da niyyar gina ƙasa da haɗin kai ba tare da rikici ko cin mutunci ga gwamnati ko shugabanni ba.

NNPP Kano
Tsagin NNPP ya ce ya kori Kwankwaso da NNPP daga tafiyarsa. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Alakar Kwankwaso da 'yan APC

Alakar siyasa tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Ganduje ta kasance mai tsami tun bayan zaben 2019, lokacin da suka yi hamayya a jam’iyyar APC a jihar Kano.

Ganduje, wanda shi ne gwamnan Kano, ya samu goyon bayan jam’iyyar APC yayin da Kwankwaso ya KOMA jam’iyyar NNPP domin neman shugabancin kasa. Wannan ya raba su, inda aka samu cikas da rashin jituwa a cikin jam’iyyar APC.

A shekarun baya-bayan nan, musamman bayan Kwankwaso ya koma NNPP, rikici ya ƙara tsananta, har aka kai ga Kwankwaso ya fuskanci korar jam’iyyar NNPP bisa wasu rigingimu.

Tsagin NNPP ya bayyana cewa Kwankwaso ba ya wakiltar jam’iyyar a hukumance, inda suka nemi afuwar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC saboda wasu kalaman Kwankwaso da suka yi barazana ko sukar gwamnati.

Ana hasashen cewa a zaben 2027, Kwankwaso na iya shiga tsagin Tinubu da APC, sai dai wasu na ganin Ganduje ka iya zama masa kadangaren bakin tulu idan ya kusanci jam'iyyar APC.

NBA ta caccaki Abba kan sanya dokar radiyo

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar lauyoyin Najeriya ta kasa NBA ta yi kakkausar suka ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan sanya doka a kafafen sadarwa.

Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana yin shirye shiryen siyasa kai tsaye a gidajen radiyon da suke fadin jihar Kano domin kare mutunci da al'adun al'umma.

Sai dai kungiyar NBA ta ce Abba Kabir ba shi da hurumin saka dokar, domin aiki ne da ke karkashin hukumar NBC ba gwamna ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »