Kwankwaso Ya Gama Yanke Shawara kan Jam'iyyar da Zai Koma kafin 2027? An Samu Bayani
- Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ƙaryata raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin sauya sheka zuwa wata jam'iyya kafin 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023 ya ce sanarwar da aka jingina masa ƙarya ce da ba ta da tushe ballantana makama
- Kwankwaso ya bukaci al'umma su daina ɗaukar kowane irin labari matukar ba daga shafukansa na sada zumunta ko wasu kafofi da ya amince da su suka fito ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Dan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata jita-jitar cewa yana shirin komawa wata jam’iyyar siyasa gabanin 2027.
Kwankwaso, jagoran NNPP na ƙasa ya nesanta kansa daga sanarwar da ake alaƙanta shi da ita cewa ya yanke shawara kan jam'iyyar da zai koma.

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tsohon gwamnan na jihar Kano ya wallafa a shafinsa na X yau Asabar, 17 ga watan Mayu, 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Rabiu Kwankwaso ya musanta jita-jitar sauya sheka
Kwankwaso ya bayyana cewa bai da wata alaka da irin wannan batu, yana mai cewa hakan ba komai ba ne illa karya da siyasar rudani da ake yi da sunansa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin cewa da yiwuwar Kwankwaso ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
A baya bayan nan nan wani mai suna, Rabiu Ibrahim ya fitar da sanarwa cewa Kwankwaso ya yanke makomar siyasarsa yayin da ake shirin tunkarar 2027.
Da gaske Kwankwaso zai shiga haɗakar su Atiku?
Da yake martani kan lamarin, Kwankwaso ya ce:
"An ja hankali ne kan wata sanarwa da ake yaɗawa da sunana cewa na yanke shawara kan abubuwan da ke faruwa a siyasar Najeriya.
"Ina tabbatar da cewa wannan sanarwa da aka jingina mani karya ce, ba ta da tushe ballantana makama, kirkirarren labarai ne na ƙarya a siyasa.
"Tuni na daina sa baki a harkokin siyasar Najeriya kuma zan ci gaba da kame baki na har zuwa wani lokaci
- Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Twitter
Kwankwaso ya ba ƴan Najeriya shawara
Tsohon gwamnan ya kuma ƙara da cewa bai taɓa sa hannu ko bada izini a fitar da kowace irin sanarwa ba dangane da batun komawa wata jam’iyya.
Madugun Kwankwasiyya ya ja hankalin jama’a da su rika duba sahihan bayanai daga shafukansa na sada zumunta kaɗai da sauran kafofin da suka dace.
Kwankwaso ya ce babu mai iya faɗa da tafiyarsa
A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya yi ikirarin cewa duk wanda ya tataro faɗa da tafuyar Kwankwasiyya to zai sha kunya.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa ya ce Kwankwasiyya ta riga ta kafa ginshikin da duk mai faɗa da ita ba zai kai labari ba.
Kwankwaso ya bayyana cewa wadanda suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC sun cin amanar wadanda suka zabe su a karkashin tutar jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng