Halin da Ake ciki bayan Faɗa Ya Kaure a Kokarin Sulhu tsakanin Masoyan Wike da Fubara

Halin da Ake ciki bayan Faɗa Ya Kaure a Kokarin Sulhu tsakanin Masoyan Wike da Fubara

  • Taron jin ra'ayin jama'a da aka yi a Port Harcourt ya rikide ya zama rikici tsakanin magoya bayan Nyesom Wike da na dakataccen Gwamna Simi Fubara
  • Shugaban GDI ya ce su ne suka taimaka wa Fubara dawowa mulki, hakan ya fusata wasu daga cikin mahalarta taron
  • Maganganu sun kara rikita taron, inda aka samu hayaniya da musayar kalamai har aka sa jami'an tsaro suka shiga tsakani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Taron jin ra'ayi da aka shirya a Port Harcourt ya rikide bayan barkewar rikici game da dokar ta-ɓaci a Rivers.

Rigimar ta kaure ne tsakanin magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike da na dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara.

An yi hatsaniya tsakanin masoyan Wike da Fubara
Faɗa ya kaure tsakanin magoya bayan Wike da Fubara. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

An yi hatsaniya tsakanin masoyan Wike da Fubara

Punch ta ce an shirya taron domin tattauna matsalolin siyasa a jihar amma ya rikice bayan mahalarta sun fara bayyana ra’ayoyinsu da karfi da yaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Takaddama ta kunno kai ne lokacin da shugaban GDI, Bright Amaewhule, ya ce su ne suka taka rawa wajen kawo Fubara mulki.

Ya ce:

“Ina ganin babu dan Rivers da bai san rawar GDI wajen kawo Fubara mulki ba.
“GDI ne suka ja hankalin jama’a su karbi Fubara, duk da an ki amincewa da shi daga 'yan uwansa na jini.”

Wannan magana ta tayar da kura, inda shugabar jam’iyyar LP, Hilda Dokubo, ta fice daga taron tana fadin, 'ba zan saurara ba'.

Sai dai daga baya masu shiryawa suka lallashe ta ta dawo cikin taron domin ci gaba da zaman jin ra’ayin jama’a a jihar.

Rikici ya sake kunno kai lokacin da wani mai jawabi, Kenwell Ibanibo, ya kalubalanci maganar Amaewhule kan kokarin tsige Fubara.

Ya ce:

“Ina tambaya, me ya sa aka so tsige Fubara bayan watanni biyar?"
An kaure tsakanin magoya bayan Wike da Fubara
Hatsaniya ta ɓarke tsakanin masoyan Wike da Fubara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kalaman da suka fusata masoyan Wike

Wannan kalamai na Ibanibo ya fusata magoya bayan Nyesom Wike, ciki har da shugaban bangaren APC, Chibike Ikenga, sai aka fara musayar kalamai.

Wani masoyin Wike ya yi ihu yana cewa:

“Ku zagi Wike yanzu! Za ku dawo ku na roƙo!”

Daga bisani, mai gabatar da taron Jake Epelle ya kasa dakile hayaniyar, sai aka kira jami’an tsaro suka dauki mataki a wajen.

Ibanibo daga karshe ya yanke shawarar barin dandalin domin rage zafin rikicin da ke kara ta’azzara a tsakanin bangarorin biyu, Channels TV ta ruwaito.

Sai dai, Ann-Kio Briggs ta sake fuskantar katsalandan daga wurin Ikenga yayin da take gabatar da nata jawabin a taron.

Ta mayar da martani da cewa:

“Ban san lokacin da ka yi magana ba. Don Allah ka barni. Ina magana da kaina ba a madadinka ba.”

Wannan rikici ya bayyana yadda siyasar jihar Rivers ke cike da rabuwar kai da rashin fahimta, duk da kokarin sulhu da ake yi.

Wike ya fadi wadanda suka raka Fubara sulhu

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da ziyarar Siminalayi Fubara tare da gwamnoni biyu na jam'iyyar APC.

Wike ya ce bai yarda Fubara na da karfin kawo zaman lafiya ba, yana sukar yadda magoya bayansa ke ci gaba da tayar da hankali.

Fubara ya bukaci magoya bayansa da su dakatar da daukar matakai da sunansa, yana cewa wasu ayyukan suna barazana ga kokarin sulhu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »