2027: APC Ta Dauki Zafi da Atiku Ya Ambato Mutanenta cikin Masu Son Kifar da Tinubu

2027: APC Ta Dauki Zafi da Atiku Ya Ambato Mutanenta cikin Masu Son Kifar da Tinubu

  • Jam’iyyar APC ta musanta ikirarin Atiku Abubakar cewa tana cikin hadakar adawa da ke shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Wannan martani ya biyo bayan Atiku ya hada APC a jerin jam’iyyun da ake son yin tafiya da su a hadakar adawa kafin babban zabe mai zuwa
  • Amma hadimin tsohon dan takarar, Paul Ibe, ya fayyace kalaman Atiku tare da bayyana abin da ya ke nufi da ambaton APC a hadakarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – APC ta mayar da martani mai zafi kan ikirarin da Atiku Abubakar ya yi cewa ‘yan jam’iyyar mai mulki suna cikin wani hadakar jam’iyyu da ke kokarin tumbuke Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Atiku ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba yayin da yake karbar bakuncin wasu jiga-jigan siyasa daga yankin Kogi ta Gabas a birnin tarayya, Abuja.

Atiku
APC ta yi martani ga kalaman Atiku a kan hadakar adawa Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Punch ta ruwaito cewa ssohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa wasu mutane daga APC, PDP, LP da sauran jam’iyyu suna cikin wannan sabuwar hadaka da nufin “ceto Najeriya.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sai dai mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya bayyana cewa Atiku yana nufin wasu mutane ne daga cikin jam’iyyar APC, ba jam’iyyar gaba ɗayanta ba.

Martanin APC ga Atiku Abubakar

A wata hira, Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya bayyana ikirarin Atiku a matsayin rudu kuma ba shu da tushe ko makama.

Bala Ibrahim ya ce:

“Ana ruɗar da Atiku. APC ba ta da wani hannu a kowace irin hadaka. A matsayinta na jam’iyya, muna da fahumtar juna, muna ƙara ƙarfi a kullum, kuma ba mu damu da wasan kwaikwayon siyasar Atiku ba.”

“Idan wani ɗan APC yana magana da shi, wata kila suna jan hankalinsa ne kawai, kamar yadda aka saba a baya. Duk lokacin da ya shiga hadaka, yana ƙarewa a rashin nasara. Wannan ne salon da aka saba da shi.”

Hadakar Atiku ta samu karuwa

A gefe guda, jam’iyyar ADC ta bayyana kanta a matsayin motar da ke dauke da sabuwar hadakar adawa a Najeriya.

Yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar a Abuja ranar Alhamis, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Nwosu, wanda shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, Mani Ahmed, ya wakilta, ya ce:

Atiku
APC ta ce babu 'ya'yanta a cikin kawance yan adawa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook
“Da ikon Allah, zan iya bayyana a fili cewa jam’iyyar ADC ce jam’iyyar hadaka a Najeriya. Abin da ya rage shi ne a kammala tattauna al’amura.”
“Kididdiga na nuna cewa kusan mutane miliyan biyar ke shiga cikin kangin talauci a kowace shekara. Wannan abin kunya ne ga ƙasa da Allah ya albarkace da arziki.”

Atiku ya ce har da APC a hadakar adawa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce shirin da wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban ke yi tasiri a zaben 2027.

Atiku ya ce akwai kawancen jam’iyyun adawa da wasu daga cikin APC da suka haɗu domin “ceto Najeriya” daga halin da tattalin arziki ya shiga a gwamnatin Bola Tinubu.

Ya fadi haka a Laraba, 14 ga Mayu, 2026 a Abuja yayin wata ziyarar manyan yan siyasa daga yankin Kogi ta Gabas karkashin tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »