An Zo Wajen: APC Ta Fadi Matsayarta kan Maida Najeriya Karkashin Jam'iyya 1
- Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar APC, ya yi tsokaci kan zargin da ake yi na shirin maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya
- Felix Morka ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki ba ta da wani shiri na ganin cewa an ƙarya ƴan adawa gaba daya a Najeriya
- Kakakin na APC yake cewa babu wani laifi idan ƴan siyasa na jam'iyyun adawa sun sauya sheƙa zuwa cikin jam'iyya mai mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya yi magana kan batun maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.
Felix Morka ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta da wata niyya ta maida Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Asali: Twitter
Felix Morka ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Arise tv a shirinsu na ‘The Morning Show’ a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
APC ta kare shigowar ƴan adawa cikinta
Sakataran yaɗa labaran ya ce sauya sheƙar da wasu ƴan jam’iyyun adawa ke yi zuwa APC ba yana nufin jam’iyyar na neman kafa tsarin jam’iyya ɗaya ba ne.
Ya ce lokacin da jam’iyyar PDP ke kan mulki, tana da iko a jihohi fiye da 28, amma babu wanda ya zarge ta da yunkurin mai da ƙasar ƙarƙashin jam’iyya ɗaya.
“Babu wani laifi idan ƴan PDP ko ƴan LP su na sauya sheƙa zuwa APC idan su na so su kasance cikin jam’iyya mai mulki."
“Yawancin waɗannan mutane suna zuwa ne suna cewa suna son su kasance cikin tsarin. Suna son su haɗa kai da wannan tafiya. Babu wani laifi a hakan."
"Kuma ka sani, hakan ba yana nufin muna da niyyar maida Najeriya ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba.”
- Felix Morka
Zama karkashin jam'iyya 1 zai yi wuya a Najeriya
Ya ƙara da cewa Najeriya ƙasa ce mai jam’iyyu da dama, kuma APC ba za ta iya saɓawa kundin tsarin mulki ba ta hanyar ƙoƙarin kafa tsarin jam’iyya ɗaya.
Ya bayyana cewa domin yin hakan dole ne an yi wa kundin tsarin mulki garambawul, wanda a cewarsa kusan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba.

Asali: Twitter
“Ƙasarmu, kamar yadda kundin tsarin mulki, dokar zaɓe da sauran dokoki da dama suka tanada, an gina ta a tsarin kasancewa mai jam’iyyu da dama."
"Saboda haka, ba za mu iya a matsayinmu na jam’iyya mu ƙi yarda da dokar kundin tsarin mulki ba mu ce muna son jam’iyya ɗaya. Domin yin hakan, sai an sauya abubuwa da dama, kuma hakan kusan ba zai yiwu ba."
- Felix Morka
Sakataren yaɗa labaran na ƙasa ya ƙaryata zargin kafa tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa abin da APC ke maida hankali a kai shi ne kare kanta da tabbatar da ci gaba da kasancewa jam’iyyar da ke jan ragamar mulki.
Yadda ake rububin shiga APC
'Yan siyasa na yawan sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a kwanakin nan, musamman daga jam’iyyun adawa.
Misali, ‘yan majalisar wakilai biyu daga Kano sun koma APC saboda rikicin cikin gida a NNPP, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.
Haka kuma, dan majalisa daga Osun, Oluwole Oke, ya koma APC a hukumance. Wannan yawan sauya sheƙa na kara karfin APC a fadin Najeriya.
Sakataren yada labarai na APC, Felix Morka, ya bayyana cewa ba laifi ba ne ‘yan siyasa su zo cikin jam’iyya mai mulki, kuma APC ba ta neman kafa tsarin jam’iyya ɗaya ba. Wannan yanayi na nuna yadda APC ke jan hankalin ‘yan siyasa kafin zaben 2027.
Sanatocin PDP sun koma APC a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sanatocin jam'iyyar PDP a jihar Kebbi, sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Sanatocin sun bayyana sauya sheƙar ta su ne a cikin wasiƙun da suka aikawa shugaban majalisar dattawa.
Tsofaffin mambobin na PDP sun danganta ficewarsu da rikicin da ya daɗe yana addabar jam'iyyar wanda aka kasa kawo ƙarshensa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng