ADC: Za a Tara Kuri'u Miliyan 35 domin Fatattakar APC da Tinubu a 2027
- Jam’iyyar ADC ta ce tana shirin tara masu kada kuri’a miliyan 35 don kawar da APC da Bola Bola Tinubu idan ya tsaya takara a 2027
- Shugaban jam’iyyar na kasa, Ralphs Okey Nwosu ne ya bayyana haka yayin wani muhimmin taron da ADC ta shirya a birnin tarayya Abuja
- ADC ta ce tana hada kai da kungiyoyin fararen hula da matasa, tare da shirin kafa babban kawance da sauran jam’iyyu domin kifar da APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Ralphs Okey Nwosu, ya caccaki jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ralphs Okey Nwosu ya yi magana yana mai cewa cin zabe da kasa da kuri’u miliyan 10 daga cikin masu rijista miliyan 88 ba abu ne da ya dace da shugabanci ba.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto Nwosu ya ce ADC na aikin sake tsari da wayar da kan al’umma domin farfado da yin zabe, musamman a tsakanin wadanda suka daina kada kuri’a saboda takaici.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Shugaban jam'iyyar ya ce:
“Zaben shugaban kasa na gaba zai kasance wanda kowa zai gane matsayinsa ba tare da wata shakka ba.”
Shirin ADC na kayar da APC da Tinubu a 2027
Jam’iyyar ta bayyana cewa a yanzu tana mayar da hankali wajen jawo sababbin masu kada kuri’a, musamman matasan da suka kai shekaru 18 tun bayan zaben 2023.
Nwosu ya ce:
“Kungiyoyin fararen hula sun riga sun shiga cikin shirinmu tun fiye da wata shida da suka wuce, kuma a yanzu suna da sama da mambobi miliyan 5.
"Sun shirya samar da kuri’u miliyan 20.”
Ya kara da cewa shirin janyo mutane miliyan 35 da suka hakura da kada kuri’a ko sababbin masu jefa kuri’a zai tabbata.
Shirin kafa babban kawance a zaben 2027
Shugaban jam’iyyar ADC ya ce suna tattaunawa da wasu jam’iyyu da kungiyoyi masu kishin kasa domin kafa babban kawance da zai hada dukkan masu son sauyi a Najeriya.
Rahoton the Guardian ya nuna cewa ya ce:
“Za ku shaida hadin gwiwa mafi girma da aka taba gani a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.
"Muna hada kai da jam’iyyu da kungiyoyi masu kishin kasa domin kafa gwamnati da al’umma za su mora kai tsaye,”

Asali: Facebook
Jam’iyyar ADC ta bukaci 'yan Najeriya su farka su nemi sauyi a 2027 ta hanyar kada kuri’a da zaben shugabannin da suka cancanta.
Oshiomhole ya ce Tinubu zai ci zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya ce Bola Tinubu zai lashe zaben 2027 ba tantama.
Sanata Adams Oshiomhole ya ce Bola Tinubu ya yi aiki tukuru a kasa da shekara biyu da ya yi a kan karaga kuma hakan zai saka a zabe shi a 2027.
Oshiomhole ya ce Bola Tinubu ya yi kokarin farfado da tattalin Najeriya musamman wajen toshe barnar da ake a bankin CBN.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng