'Ka da Ka Raina El Rufai': Malami Ya Gargadi Tinubu, Ya Magantu kan Sauya Shettima
- Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Bola Tinubu game da Nasir El-Rufai, ya ce yana shirin kara kaimi domin kalubalantarsa a 2027
- Malamin addinin ya ce duk da matsaloli za su taso tsakaninsu, Tinubu bai kamata ya sauya mataimakinsa Kashim Shettima ba
- Hakan ya biyo bayan tuntubar manyan 'yan siyasa a fadin kasar da El-Rufai ke yi domin shiri a zaben 2027 da kalubalantar Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fitaccen malamin addini, Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana wani hasashe dangane da zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Fasto Ayodele, wanda aka fi sani da yin hasashe, ya bayyana abin da ya hango game da babban zaben gaba a Najeriya.

Asali: Facebook
An shawarci Tinubu game da El-Rufai
A cikin wata hira da Tribune, malamin ya yi hasashe kan makomar siyasar Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Kashim Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ayodele ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ka da ya raina tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Shugaban cocin 'INRI Evangelical Spiritual' ya ce El-Rufai na shirin fafatawa mai karfi.
Ayodele ya shawarci Shugaba Tinubu da ya kasance cikin shiri domin matsalolin da zai fuskanta.
Malamin da ke zaune a Lagos ya ce:
"Game da El-Rufai, ka da ka raina shi, ya na shirin fafatawa mai karfi, dole ne ka yi shiri."

Asali: Facebook
Tasirin Nasir El-Rufai a zaben 2027
El-Rufai na iya zama wanda ke jagorantar yunkurin hana Tinubu wa’adi na biyu a 2027.
Bayan sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP, El-Rufai ya fara taka rawar gani a matsayin jigo na adawa.
Haka kuma, El-Rufai ya taka rawa wajen shawo kan gwamnonin Arewa su goyi bayan Tinubu a zaben fidda gwani na APC.
A zahiri, El-Rufai wanda ya yaki jam'iyyar LP da Peter Obi a zaben 2023, ya fara kusantarsa saboda 2027.
A baya-bayan nan, su biyun sun gana a Amurka yayin taron 'Cambridge Africa Together' karo na 11 da aka yi a jami’ar Cambridge.
El-Rufai yana cikin wadanda suka gabatar da jawabi a taron da aka hada shugabanni, masana da masu sauya al’amura daga Afirka.
Fasto ya gargadi Tinubu kan sauya Shettima
Dangane da mataimakin shugaban kasa, Ayodele ya bukaci Tinubu ka da ya sauya Kashim Shettima.
Malamin ya ce:
"Eh, za su samu matsaloli, amma dole ne ya bar Shettima ya kammala wa’adinsa. Wannan shi ne shawara ta."
Fasto ya yi hasashe game da zaben 2027
Kun ji cewa Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya yi tsokaci mai zafi kan zaben 2027, ya ce zaɓen Peter Obi ko Atiku Abubakar hatsari ne matuƙa.
Ayodele ya ce Allah ya nuna masa mutane uku da za su hana Bola Tinubu samun nasara a 2027 idan ɗaya daga cikinsu ya fito takara.
Faston ya ja kunnen Tinubu game da lamarin mataimakinsa, Kashim Shettima duba da rade-radin da ake yaɗawa cewa zai rabu da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng