Sanata Ya Tsage Gaskiya kan Batun Tinubu na Tilastawa 'Yan Adawa Komawa APC
- Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamdele, ya kare mai girma Bola Tinubu kan zargin tilastawa ƴan adawa komawa APC
- Sanata Bamdele ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai tilastawa ƴan adawa shigowa jam'iyyar APC mai mulki da rinjaye a majalisar kasa
- Ya nuna cewa APC ba irin jam'iyyar PDP ba ce wacce a lokacin mulkinta ta riƙa ƙoƙarin ƙara yawan jihohin da take da iko da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya yi magana kan sauya sheƙar ƴan adawa zuwa APC.
Opeyemi Bamidele ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya tilastawa ƴan majalisa na jam'iyyun adawa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ranar Talata, yayin da yake kare sauya shekar da sanatocin PDP uku daga jihar Kebbi suka yi zuwa APC, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sanata Bamidele ya kare jam'iyyar APC
Bamidele ya jaddada cewa jam’iyyar APC da ke mulki yanzu tana tafiyar da gwamnatin haɗin kan ƙasa, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
Ya bayyana cewa sauya sheƙar da sanatocin na PDP suka yi ba wani yunƙuri bane na juyar da Najeriya zuwa ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.
Waɗanda suka sauya sheƙar sune, Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Sanata Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu).
A cewarsa, jam’iyyar APC ba za ta rufe kofa ga kowane mutum da ke da niyyar shiga cikinta ba.
"Haka kuma, ba za mu nuna wariya ga kowa ba, ko saboda addini, ko ƙabila, ko wani dalili. Kofofinmu za su ci gaba da kasancewa a buɗe ga duk wanda ke son shigowa, a kowane mataki."
"A halin yanzu, za mu ci gaba da aiki tare da mambobin jam’iyyun adawa.”
- Opeyemi Bamidele
Shin ana tilastawa ƴan adawa komawa APC?
Bamidele ya yabawa ƴan majalisar da suka sauya sheƙa zuwa APC, inda ya kwatanta hakan da lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki, tana tilastawa mambobin jam’iyyun adawa shiga cikinta.

Asali: Facebook
"Mun kasance a wannan ƙasa lokacin da PDP ke mulki. Mun shaida abubuwan da suka faru ƙarƙashin PDP, yanda suke ƙoƙarin samun ƙarin jihohi, ƙarin kujeru a majalisar dattawa da majalisar wakilai.”
"Yanzu ba lokacin zaɓe ba ne. Babu wanda ake tilastawa. Idan ana tilastawa wani, tabbas ba Sanata Adamu Aliero bane. Kowa ya san cewa Sanata Yahaya Abdullahi ba wanda za a tilastawa shiga wata jam’iyya bane"
"Haka kuma Sanata Garba Maidoki ba zai kasance wanda za a tilastawa sauya sheƙa zuwa APC ba tare da ya gamsu da hakan ba."
- Opeyemi Bamidele
PDP ta magantu kan komawar sanatocinta APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta yi martani kan ficewar sanatocinta guda uku zuwa APC.
Shugaban PDP na jihar, Usman Bello Suru, ya bayyana cewa ficewar sanatocin ba za ta sanya ƙarfi da tasirin da jam'iyyar take da shi ya ragu ba.
Hakazalika, ya zargi sanatocin da cin amanar jam'iyyar PDP duba da irin gatan da ta yi musu lokacin da APC ta hana su takara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng