'Ka Rubuta Littafin Sauya Sheka,' Oshiomole Ya Tsokano Atiku kan Yawan Canza Jam'iyyu

'Ka Rubuta Littafin Sauya Sheka,' Oshiomole Ya Tsokano Atiku kan Yawan Canza Jam'iyyu

  • Tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya ce Atiku Abubakar ne ya fara sauya shekaa daga jam’iyya mafi shahara a tarihin Najeriya
  • Ya ce a lokacin da Atiku ya bar PDP ya koma ACN a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, lamarin ya ba da mamaki matuka
  • Oshiomhole ya bukaci Atiku ya rubuta littafi da zai bayyana dalilin da yasa ‘yan siyasa ke sauya jam’iyya daga lokaci zuwa lokaci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Adams Oshiomhole, Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya rubuta littafi kan sauya sheka.

Oshiomhole ya ce sauya sheƙar Atiku daga PDP zuwa ACN a lokacin yana rike da matsayin mataimakin shugaban kasa na daya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasar Najeriya.

Adams
Oshiomhole ya kalubalanci Atiku kan sauya sheka Hoto: Adams Oshiomhole/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Edo ya bayyana hakan ne a cikin shirin Politics Today da aka gudanar kai tsaye ta Channels Television a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Oshiomhole ya soki Atiku bisa yawan sauya jam’iyya

Jaridar Vanguard News ta ruwaito cewa Oshiomhole ya ce babu wani ɗan siyasa da ya sauya jam’iyya da yawa kamar Atiku Abubakar.

Ya ce:

“Bari in tunatar da ku, cewa wanda ya fara wannan al’ada ta sauya jam’iyya — mafi shahara a tarihin Najeriya — shi ne mai girma Atiku Abubakar.
“A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa a wancan lokaci, ya bar PDP ya koma ACN — wadda yanzu ta zama bangare na APC. Shin tursasa masa aka yi?

Oshiomhole ya yi martani ga masu sukar APC

Oshiomhole ya kalubalanci masu cewa babu daidaito ko akwai wata matsala a cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Sanatan na Edo ta Arewa ya kuma tambaya ko akwai wanda ya tilasta wa Atiku komawa PDP bayan faduwarsa a zaben shugaban kasa karkashin APC.

Atiku
Oshiomhole ya ce Atiku ne ya bude kofar sauya sheka mafi girma a tarihi Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

“Shin mu ne muka tilasta masa ya fice daga jam’iyyarmu ya koma PDP domin ya kara takara da Jonathan?”
“Da ya sha kaye, mu ne muka tilasta masa — duk da ba muna mulki ba — ya dawo APC ya kara da Buhari?
“Na yi imanin mutumin da ya fi cancanta ya rubuta littafi kan dalilin sauya jam’iyya a Najeriya, ba wani bane illa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
“Ya kamata a tambaye shi: a matsayinka na mataimakin shugaban kasa, ka fice daga jam’iyyarka, me ya janyo hakan?”

Atiku Abubakar ya rike matsayin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma tarihin siyasar sa cike take da sauya jam’iyya na daga cikin abin da ke jawo cece-kuce.

Atiku ya caccaki Tinubu da EFCC

A baya, mun wallafa cewa Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumar EFCC ke ci gaba da cafke mutane ba tare da bin ka’ida ba a kasar nan.

Atiku ya nuna bakin ciki kan cafke tsohon dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure, a Kano, aka wuce da shi Abuja ba tare da wani bayani ba.

Ya ce kama Hon. Kazaure ba tare da bayani ba, na nuni da rashin bin doka da kuma yunkurin dakile ’yancin fadin albarkacin baki da doka ta ba da dama a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »