Bukola Saraki da Mutane 7 Za Su Kawo Karshen Rikicin PDP, An Ji Shirin da Suka Yi

Bukola Saraki da Mutane 7 Za Su Kawo Karshen Rikicin PDP, An Ji Shirin da Suka Yi

  • Bukola Saraki zai jagoranci kwamitin mutane bakwai da zai dinke barakar da ke cikin jam'iyyar PDP don tunkarar zaɓen 2027
  • Kwamitin da aka kafa shi a yayin wani taron gwamnonin PDP, zai tabbatar da taron NEC da babban taron ƙasa sun gudana cikin nasara
  • Saraki, wanda ya yi alkawarin dawo da martabar PDP, ya ce kwamitinsa ya kunshi gwamnoni masu ci uku da tsofaffin gwamnoni uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki zai jagoranci kwamiti na musamman da zai dinke barakar PDP da shirya ta don tunkarar zaben 2027.

Kwamitin, wanda Saraki zai jagoranta, ya ƙunshi gwamnoni uku masu ci; Dauda Lawal na Zamfara, Caleb Muftwang na Filato, da Peter Mbah na Enugu, da kuma tsofaffin gwamnoni uku: Seriake Dickson, Ibrahim Dankwambo, da Okezie Ikpeazu.

Jam'iyyar PDP ta nada Saraki a matsayin shugaban kwamitin sulhu gabanin taron NEC
Taron jiga-jigan jam'iyyar PDP da ya gudana a gidan gwamnatin Bauchi da ke Abuja. Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Vangaurd ta rahoto cewa kwamitin zai yi duk mai yiwu wa don ganin taron NEC na PDP ya gudana cikin nasara a ranar 27 ga Mayu da kuma babban taron ƙasa mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Saraki zai jagoranci kwamitin dinke barakar PDP

An kafa kwamitin ne a wani babban taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Bauchi da ke Abuja, inda gwamnonin PDP masu ci da tsofaffi suka halarta.

Taron ya nuna ƙudurin jam'iyyar na warware matsalolin cikin gida da ƙarfafa matsayinta na gabanin manyan al'amuran siyasa da ke tunkar ƙasar nan.

Ayyukan kwamitin Saraki sun hada da ɗinke barakar da ke tsakanin ɓangarori daban-daban na jam'iyyar tare da dawo da hadin kai don shirya wa zaɓuka masu zuwa.

Ana ganin wannan wani babban mataki ne da zai iya gyara siyasar PDP domin ganin ta samu nasara a zaɓukan 2027.

Abin da Bukola Saraki ya ce kan taron PDP

Da yake magana a Abuja bayan taron kungiyar gwamnonin PDP da aka faɗaɗa, Saraki ya jaddada mahimmancin haɗin kai a cikin jam'iyyar.

Bukola Saraki ya ce:

"An kammala taron kungiyar gwamnonin PDP, inda gwamnoni masu ci da tsofaffi suka halarta, a gidan gwamnatin Bauchi.
"Mun yi muhawara mai ma'ana kan ƙalubalen da jam'iyyar ke fuskanta a halin yanzu da kuma alkiblarta na gaba."

Tsohon shugaban majalisar ya jaddada ƙudurin kwamitin dabaru da tsare-tsare da aka ba shi jagoranci na warware sabanin da ke a jam'iyyar da samar da hanya madaidaiciya ga PDP.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Saraki yana cewa:

"A matsayin wani ɓangare na shawarwarin da aka ɗauka, an kafa kwamitin dabaru da tsare-tsare mai mambobi bakwai da aka ɗorawa alhakin shirya taron NEC a ranar 27 ga Mayu da kuma babban taron ƙasa mai zuwa."
Saraki ya jaddada kudurin kwamitin sulhu da zai jagoranta na kawo karshen rikicin PDP
An nada Saraki shugaban kwamitin sulhu a taron PDP da ya gudana a Abuja. Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Tasirin kwamitin da Saraki ke jagoranta

Saraki ya nuna kyakkyawan yakini game da ayyukan kwamitin, yana mai cewa, "Mun ƙudurta yin iya ƙoƙarinmu don sauke nauyin da aka ɗora mana."

Ana kallon taron NEC na PDP mai zuwa da kuma babban taron jam'iyyar na ƙasa a matsayin muhimman tarurruka da za su su tsara muhimman muƙaman shugabanci da zaben ƴan takara, wanda zai ƙayyade shirye-shiryen jam'iyyar don zaɓukan gaba.

Ƙoƙarin kwamitin da Saraki ke jagoranta, tare da goyon bayan manyan jiga-jigan siyasa, zai kai ga haɗin kai da kuma dawo da karfin siyasar PDP a Najeriya.

Abin da ya hana PDP daukar mataki kan Wike

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban PDP na jihar Anambra, Cif Ndubuisi Nwobu, ya zargi Nyesom Wike da raba kan jam'iyyar ta hanyar goyon bayan APC.

Nwobu ya ce, Wike ya samu gagarumin tasiri a PDP tun lokacin da yake gwamna, inda ya sanya magoya bayansa a muhimman muƙamai a jam'iyyar.

Ya kuma bayyana cewa, rashin ɗaukar mataki a kan Wike ya samo asali ne daga yadda yake da rinjaye a jam'iyyar, musamman a tsakanin shugabannin da ke goyon bayansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »