Dabarun da Tinunu Ke Yi domin Nakasa Atiku, Obi a Jihohi 5 Kafin Zaɓen 2027

Dabarun da Tinunu Ke Yi domin Nakasa Atiku, Obi a Jihohi 5 Kafin Zaɓen 2027

  • Shugaba Bola Tinubu na kokarin kafa tubali a yankin Kudu maso Gabas don samun nasara a zaben 2027 da kayar da Atiku Abubakar da Peter Obi
  • Tinubu ya ziyarci jihohin da ba na jam'iyyarsa ba tare da gina kawance da gwamnoni, ciki har da na LP da PDP, yana samun karbuwa sosai
  • A Anambra, Gwamna Soludo ya mara masa baya, APGA ta ce zai zama dan takararsu na 2027, duk da kasancewar jihar asalin ta Obi ce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya dauki wata hanya domin nakasa Atiku Abubakar da Peter Obi a wasu jihohi biyar a Najeriya.

Tinubu na kokarin keta yankin Kudu maso Gabas da kayar da abokan hamayyarsa, Atiku da Obi, kafin zaben 2027.

Shirin Tinubu kan Atiku, Obi a 2027
Shirin Tinunu kan Atiku, Obi a jihohi 5. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu, Peter Obi.
Asali: Facebook

2027: Tinubu na babban shiri a jihohi 5

Shugaban na iya hango hadin guiwar da ke iya shiga tsakanin Atiku da Obi, lashe Kudu maso Gabas zai zama babbar nasara gare shi, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yayin da jihohi biyu cikin biyar na yankin ke karkashin APC, shugaba Tinubu ya fara kafa kawance da gwamnoni uku na sauran jihohin.

Shugaba Bola Tinubu na fuskantar barazana mai tsanani a kokarinsa na tazarce a 2027 saboda Atiku da Obi na hada kai don hambarar da shi.

A 2023, Atiku da Obi sun samu kuri’u sama da miliyan shida kowannensu, yayin da Tinubu ya samu sama da miliyan takwas a zaben shugaban kasa.

Saboda haka, ana kallon hadin kan Atiku da Obi a matsayin barazana da ka iya kifar da shugaba Tinubu a 2027.

Tinubu, wanda ake kira da kwararren dan siyasa, yana tsara dabarun da za su taimaka masa sake lashe zabe da hana 'yan adawa cimma nasara.

Daya daga cikin dabarunsa ita ce shigowa yankin Kudu maso Gabas a 2027, yankin da ake kallon Obi a matsayin gwarzo kuma mai karbuwa.

Tasirin Obi a yankin Kudu maso Gabas

A zaben baya, Obi ya samu kusan kashi dari cikin dari na kuri’u a yankin, don haka Tinubu ke kokarin karya masa wannan tasiri.

Ya karfafa dangantaka da gwamnoni na Kudu maso Gabas, musamman wadanda ke jam’iyyun adawa, inda ake ganin yana kokarin shawo kansu.

A ranar 27 ga Fabrairu, 2024, Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilce shi a Abia, inda ya yaba wa Gwamna Alex Oti na LP.

Haka kuma, a watan Janairu, shugaban kasa ya kai ziyara Enugu inda ya yabawa Gwamna Peter Mbah na jam’iyyar PDP bayan bude wasu ayyuka.

Tinubu ya fara shirin nakasa Atiku, Obi
Tinubu na shirin zaben 2027 a jihohi 5 kan Atiku, Obi. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

2027: Muhimmancin ziyarar Tinubu a Anambra

A ranar Alhamis, 8 ga Mayu, ya je Anambra, inda Gwamna Soludo ya mara masa baya, yana mai cewa APGA ta yarda da shi a matsayin dan takara, cewar Premium Times.

Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya samu sarautar gargajiya ta "Dike Si Mba" daga sarakunan Anambra kafin zaben 2027.

Wannan na nufin "Jarumin da ya fito daga wata kasa", jihar da take asalin ta Peter Obi, babban abokin hamayyar Tinubu a siyasa.

Fasto ya gargadi zaben Atiku, Obi

Kun ji cewa Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya yi magana kan zaben 2027, inda ya ce zaɓen Peter Obi ko Atiku Abubakar hatsari ne.

Ayodele ya ce Allah ya nuna masa mutane uku da za su hana Bola Tinubu samun nasara a 2027 idan ɗaya daga cikinsu ya fito takara.

Faston ya ja kunnen Tinubu kada ya sauya Kashim Shettima, inda ya ce duk da matsaloli, dole ne ya kammala wa'adinsa a ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »