'Mutum 3 Za Su ba Tinubu Matsala': Malamin addini Ya ce Akwai Hatsari Zaɓen Atiku, Obi
- Fitaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya yi tsokaci mai zafi kan zaben 2027, inda ya ce zaɓen Peter Obi ko Atiku Abubakar hatsari ne matuƙa
- Ayodele ya ce Allah ya nuna masa mutane uku da za su hana Bola Tinubu samun nasara a 2027 idan ɗaya daga cikinsu ya fito takara
- Faston ya ja kunnen Tinubu kada ya sauya Kashim Shettima, inda ya ce duk da matsaloli, dole ne ya kammala wa'adinsa a ofis
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fitaccen Fasto mai hasashe a lamuran Najeriya ya sake magana kan zaben 2027 da ke tafe.
Fasto Elijah Ayodele ya yi gargadi mai zafi ga ƴan Najeriya kan zaben tumun dare a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Zaben Atiku, Obi: Fasto ya gargadi yan Najeriya
Faston ya yi wannan magana ne yayin hira ta musamman da gidan jaridar Tribune a jiya Asabar 10 ga watan Mayun 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Malamin ya ce babban kuskure da yan Najeriya za su yi shi ne zaben Peter Obi ko Atiku Abubakar a 2027.
Ya ce masifa za ta afku a Najeriya idan aka yi kuskuren zaben dan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi.
Ya kara da cewa kasar za ta rushe ne baki daya idan har yan kasar suka yi kuskuren zaben Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa.
Ya ce:
"Bari in yi bayani a fili, idan ‘yan Najeriya suka zaɓi Peter Obi, masifa za ta afkawa ƙasa nan.
"Idan kuma suka zaɓi Atiku Abubakar, Najeriya za ta rushe, duk da abin mamaki ne, Tinubu shi ɗin nan ɗaya shi ne ya kamata a zaɓa, wannan gaskiya ce."

Asali: Facebook
Fasto ya shawarci Tinubu game da Kashim
Fasto ya ce tabbas akwai wasu mutane uku da su kadai ne za su hana Bola Tinubu sakat a 2027 idan suka fito.
Ya kara da cewa:
"Da gaske ne, kwai alamar rubutu, wata irin dakatawa daga sama, Allah ya bayyana mini sunaye uku, idan ɗaya daga cikinsu ya shiga takara, shugabancin Tinubu ba zai wuce 2027 ba.
"Ba zai dawo ba amma ba zan faɗi waɗannan sunaye ba ko da an saka mani bindiga.
"Da zarar ɗaya ya fito fili, zan faɗa wa ‘yan Najeriya da ƙarfi, cewa wannan shi ne mutumin kuma Tinubu ba zai yi nasara ba."
Elijah Ayodele ya tabo maganar Kashim Shettima a matsayin mataimaki inda ya gargadi Tinubu kan kokarin sauya shi.
"Bai kamata Tinubu ya maye gurbin Shettima ba. Eh, za su fuskanci matsaloli.
"Amma dole ne ya bar Shettima ya kammala wa'adinsa. Wannan shi ne shawarar da nake ba shi."
Ribadu ne zai gaji kujerar Tinubu a 2031
Mun ba ku labarin cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi magana kan siyasar Najeriya.
Ayodele ya bayyana cewa Nuhu Ribadu zai gaji Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2031 bayan ya kammala wa'adinsa na biyu.
Malamin addinin ya ja kunnen ƴan Najeriya kan su yi taka tsantsan da ƴan siyasar da ke ƙoƙarin kafa haɗakar ƴan adawa.
Asali: Legit.ng