Alƙawarin da Ganduje Ya Yi bayan Sanatoci 3 Sun Yi Fatali da Jam'iyyunsu Zuwa APC

Alƙawarin da Ganduje Ya Yi bayan Sanatoci 3 Sun Yi Fatali da Jam'iyyunsu Zuwa APC

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya tabbatar da cewa za a karbi sababbin Sanatoci da suka sauya sheka cikin lumana da doka
  • Dr. Ganduje ya ce sauya shekar sanatan Kebbi guda uku sakamakon tuntuba ne na makonni, kuma za a sanar da sauya shekar a zauren Majalisa
  • Ya ce wannan mataki yana nuna karfin jagorancin Bola Tinubu, kuma yaduwar sauya shekar zuwa jam’iyya mai mulki ba matsala ba ce

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC na ci gaba da karɓar sababbin tuba zuwa cikinta a yan kwanakin nan.

Jam'iyyar ta samu karuwa da manyan yan siyasa ciki har da gwamna da tsohon gwamna da yan majalisu.

Ganduje ya magantu kan masu shiga APC
Ganduje ya yi alkawari ga masu komawa APC. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Ganduje ya jaddada karfin APC a Najeriya

Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa karbar sababbin sanatoci za ta gudana bisa doka da tsari, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yayin da yake magana da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa bayan ya kai sabbin ‘yan majalisar wurin Bola Tinubu, Ganduje ya ce APC jam’iyya ce mai tsari.

Ya ce:

"Dokarmu ta jam’iyya ta fayyace hakan, kuma muna da hikima ta siyasa wajen gudanar da irin wadannan al’amura."
"Don haka ina tabbatar muku da cewa za su samu karbuwa kuma ba tare da matsala ba."

Wannan ya biyo bayan sauya shekar Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abdullahi (Kebbi Arewa) da Garba Maidoki (Kebbi Kudu) daga PDP.

Ganduje ya bayyana cewa za a sanar da sauya shekar tasu a zauren majalisar dattawa cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Ya kara da cewa:

“Ranar Talata za ku ga abin da zai faru a zauren dattawa."

Ganduje ya ce sauya shekar na da tsari, kuma ya biyo bayan doguwar tattaunawa da suka yi ta bayan fage karkashin Bola Tinubu.

“Wannan bangare ne na hangen nesan shugaban kasa cewa APC ta karfafa kanta da dimokuradiyya wajen kara yawan mambobi masu inganci."

- Cewar Ganduje

Ganduje ya fadi shirin APC a Najeriya
Ganduje ya jaddada tsarin APC a mulkin Najeriya. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Twitter

Ganduje ya magantu kan tsarin jam'iyya 1

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya karbi wannan matakai hannu bibbiyu tare da amincewa da shigarsu jam’iyyar, cewar rahoton Thisday.

Dangane da fargabar cewa hakan na iya jefa kasar cikin jam’iyya daya, Ganduje ya musanta hakan da cewa hakan dimokuradiyya ce.

Yayin da ya kawo misalin China, Ganduje ya ce kasar na da karfin tattalin arziki kuma tana da jam’iyya daya; ba muna goyon bayan hakan ba.

Ganduje ya sake jaddada cewa APC na nan daram wajen dimokuradiyya, kuma duk sababbin ‘ya’ya za su samu matsayi a cikin tsarin jam’iyyar.

Yan majalisa daga PDP sun koma APC

Kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Katsina ta rasa wasu daga cikin mambobinta da ke majalisar wakilan Najeriya.

'Yan majalisar wakilan guda uku sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar a zauren majalisa a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2025.

Tsofaffin 'yan PDP da suka koma APC sun bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikicin cikin gida da take fama da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »