Magana Ta Kare, Sanatan NNPP daga Kano Ya Bar Layin Kwankwaso, Ya Koma APC
- Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa ya sanar da sauya shekarsa daga NNPP zuwa APC a hukumance
- Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar sauya sheƙar Kawu a zaman sanatoci na yau Laraba
- A wasiƙar, Sanata Kawu ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya raba kan ƴan NNPP ne ya tilasta masa ficewa daga jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Kawu Samaila, ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar da komawa APC a hukumance a wata wasiƙa da ya miƙa Majalisar Dattawa yau Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025.

Asali: Twitter
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar Kawu a zauren majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sanatocin APC sun yi maraba da Kawu
Bayan karanta wasikar, Sanatocin APC sun nuna tsantsar murna, farin ciki da maraba da Kawu zuwa inuwar jam'iyya mai mulki.
Rahoto ya nuna cewa sanatocin sun yi wa Kawu Sumaila rakiya zuwa sabuwar kujerarsa da ke gefen jam’iyya mai rinjaye a majalisar.
A cikin wasikar da Akpabio ya karanta yau Laraba, Sanata Kawu ya bayyana cewa ya bar NNPP ne bisa wasu “muhimman dalilai."
Meyasa Kawu Sumaila ya bar NNPP?
Sanatan ya ce ya yanke shawarar raba gari da NNPP ne saboda wasu "sababbin abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar da ba zai iya jurewa ba.”
Kawu, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin majalisa, ya ce NNPP ta rikide zuwa jam'iyyar rikici, rabuwar kai da rashin daidaito.
“A cikin ‘yan watannin da suka gabata, rikice-rikicen shari’a sun tarwatsa jam’iyyar tare da raunana tsarin mulkinta.
"Waɗannan rigingimu da ke gaban kotu sun haifar da rashin daidaito a cikin gida da kuma darewar shugabanci zuwa gida daban-daban, kuma kowane ɓangare na nuna shi ne halastacce."
- Sanata Kawu Sumaila.

Asali: Facebook
Sanata Kawu ya ce NNPP ta faɗa rikici
Sanatan ya kara da cewa tsohuwar jam'iyyarsa watau NNPP ta rabu gida-gida kuma kowane ɓangare yana da shugabanni.
A cewarsa, wannan ne babban dalilin da ya sa ya ga cewa ya dace ya tattara kayansa ya koma APC mai mulki.
A watan Mayu na shekarar 2022, Kawu Samaila ya bar jam’iyyar APC zuwa NNPP, kafin yanzu da ya sake dawowa APC, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A cewar wani jigo a jam'iyyar NNPP, bai yi mamaki ba da aka ce Kawu Sumaila ya bar jam'iyyar zuwa APC saboda daga can ya fito.
Da yake tsokaci kan ci gaba a wata hira da Legit Hausa, Aminu Sule ya ce dama kasuwar bukata ce ta kawo Kawu NNPP kuma ya cika burinsa ya barta.
Ɗan kwankwasiyyar ya ce:
"Ko kaɗan ban yi mamaki ba, saboda Kawu Sumaila ba don mutane yake siyasa ba, tun farko na yi tunanin mulki kawai yake so shiyasa ya dawo NNPP tun da APC ta hana shi takara.
"Yanzu ya samu abin da yake so kuma ya fita, mu dai muna nan daram a NNPP da Kwankwadiyya, idan kaga mun fita to madugu ne ya fita, wannan ce matsalarmu."
APC ta ƙara karɓar jiga-jigai a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon na hannun daman jagoran NNPP, Kwankwaso kuma jigo a siyasar Kano, Yunusa Adamu Dangwani ya sauya sheƙa zuwa APC.
Ɗangwani ya jagoranci mambobin jam'iyyar PDP da dama zuwa APC a wani taro na musamman da aka shirya domin tarbarsu a Kano.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar shugabanni da jiga-jigan jam'iyya domin maraba da masu sauya sheƙar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng