Abba Ya Jaddada Mubaya'a bayan Zargin ga Kwankwaso da Karbar Kudi a Asusun Kano

Abba Ya Jaddada Mubaya'a bayan Zargin ga Kwankwaso da Karbar Kudi a Asusun Kano

  • Bichi ya zargi Abba da badakal a gwamnatiaddada cikakkiyar biyayya da goyon baya ga jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Abba Kabir ya bayyana cewa ko ina Rabiu Kwankwaso ya dosa a siyasa, shi da mabiyansa za su bishi ba tare da wata rarrabuwar kawuna ba
  • Wannan furuci na zuwa ne bayan da wasu suka yi kiraye-kirayen cewa lokaci ya yi da Abba zai balle daga Kwankwasiyya ta tsaya da kafar shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya jaddada biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da kansiloli 484 da aka zaba daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano a fadar gwamnatin jihar.

Kwankwaso
Abba ya jaddada muba'aya ga Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa gwamnan ya jaddada muba'a a ga Kwankwaso ne a lokacin da sakataren gwamnatin jihar da aka kora ya zarge shi da karbar kudi a asusun Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A cewar Abba Kabir, gwamnatinsa na tafiya cikin gaskiya da rikon amana, kuma tana kula da duk wani abu da zai kawo ci gaba ga jihar Kano da al’ummarta.

Abba ya ce za su yi wa Kwankwaso biyayya

Gwamnan ya ce babu wani yunkuri da zai sa ya rabu da Kwankwaso, domin shi ne ya ba shi dama, ya jagorance shi tun farko, kuma har yanzu yana da daraja a idonsa da na mabiyansa.

The Guardian ta wallafa cewa Abba Kabir ya ce:

“Ina so in bayyana a fili cewa ko ina Kwankwaso ya dosa a siyasa, ni da mabiya na za mu bi shi. Shi ne jagoranmu, kuma mun yarda da shugabancinsa,”

Ya ce zargin da ake yi cewa ana bai wa Kwankwaso N2bn kowane wata bita da kulli ne daga bakin wasu ‘yan siyasar da suka rasa farin jini a idanun jama’a.

Siyasar bijirewa uban gida a Kano

A bisa maganganun da ya yi, Abba Kabir ya nuna cewa ba zai balle daga tafiyar Kwankwasiyya ba kamar yadda hakan ta faru a baya a jihar Kano.

Tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya balle daga Kwankwasiyya bayan lashe zaben gwamna a 2015.

Ana ganin ballewar da Ganduje ya yi daga tafiyar Kwankwasiyya ta jawo rashin jituwa tsakanin shi da Kwankwaso wanda hakan ya jawo ci baya ga jihar Kano sosai.

A kwanakin baya ma an fito da sabon salon kiran Abba tsaya da kafarka domin bijirewa Kwankwaso amma yaki.

Kiran Abba na zaman lafiya a jihar Kano

Gwamnan ya shawarci jama’ar Kano da su yi watsi da abin da ya kira “hayaniyar ‘yan siyasar da ba su da tasiri”, yana mai cewa gwamnatinsa na kokarin ganin Kano ta ci gaba.

Abba ya yi alkawari cigaba da ayyukan alheri da za su kawo cigaba a jihar Kano har zuwa karshen mulkinsa.

Abba Kabir
Abba ya yi alkawarin cigaba da ayyuka a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Bichi ya zargi Abba da badakala a gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi ya zargi Abba da ba daidai ba.

Dr Baffa Bichi ya ce akwai munanan abubuwa da suka faru a gwamnatin Abba Gida Gida da zai bayyana a gaba kadan.

Baya ga haka, Dr Bichi ya ce barnar da Abba Kabir ya yi ta wuce irin abin da ya faru a lokacin gwamna Abdullahi Ganduje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »