Wike Ya Zargi Gwamna Fubara da Jawo Wulakanta Matar Tinubu a Rivers

Wike Ya Zargi Gwamna Fubara da Jawo Wulakanta Matar Tinubu a Rivers

  • Ministan Abuja ya bayyana ficewar wasu mata daga wurin taron da Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, ta jagoranta a matsayin abin kunya
  • Nyesom Wike ya ce hakan rashin girmama ofishin shugaban kasa ne, yana mai neman afuwar Bola Tinubu bisa lamarin da ya faru a jihar Ribas
  • Lamari ya auku ne yayin wani taron tallafa wa mata da ofishin Uwargidar Shugaban Kasa ya shirya, wasu mata suka fice daga wurin suna zanga-zanga

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Nyesom Wike, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a China ya nuna takaicinsa kan lamarin da ya kira “abin kunya” kan zargin wulakanta matar Bola Tinubu a Rivers.

Mata sun watse a wajen taron da ofishin uwargidan shugaban kasa ta shirya a jihar domin nuna adawa da dakatar da gwamna Simi Fubara.

Fubara
Wike ya zargi Fubara kan watsewar mata wajen taron matar Tinubu. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

A wata sanarwa da hadiminsa, Lere Olayinka, ya wallafa a X, Wike ya yi Allah-wadai da ficewar wadannan mata daga taron da Uwargidar Shugaban Kasa ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Tun a karon farko dai an shirya taron ne domin tallafa wa mata 500 da suka fito daga sassa daban daban na jihar Rivers.

Sanarwar ta yi zargin cewa matan sun samu jagorancin wasu mata da aka tsige daga mukaman mataimakan shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Sakon Tinubu ga Fubara kan matar Tinubu

A cewar Wike, rashin girmama duk wanda ke wakiltar Uwargidar Shugaban Kasa tamkar cin mutuncin ofishin shugaban kasa ne gaba daya.

Punch ta wallafa cewa Wike ya ce:

“Ina rokon gafara a madadin al’ummar jihar Rivers kan wannan abin kunya da ya auku. Wannan ba dabi’ar mutanen jihar Rivers ba ce,”

Ya bukaci Gwamna Fubara da ya fuskanci gaskiya, ya bayyana wa shugaban kasa abin da yake nema kai tsaye, maimakon cewa abu guda yau, sai kuma ya yi akasin sa gobe.

Wike ya kara da cewa:

“Bai kamata mutum yana yawo yana cewa yana neman zaman lafiya, amma yana daukar nauyin mutane don su ci mutuncin shugaban kasa da matarsa ba”

Wike ya yi kira ga magoya bayan Fubara

Wike ya ce irin wadannan abubuwa da ake yi da sunan neman zaman lafiya ba za su kawo daidaito a jihar ba, domin ba a yin su da gaskiya.

Ya ce shi da mabiyansa na siyasa sun yi tir da ficewa daga taron da aka shirya don amfanin mata a jihar, yana mai cewa hakan ba ya nuna gaskiyar halayen al’ummar jihar Rivers.

Wike Abuja
Wike ya gargadi magoya bayan Fubara. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Wike ya kuma bukaci magoya bayan gwamna Fubara da su daina bata sunan jihar ta hanyar daukar nauyin abubuwan da ke zubar da mutuncinta a idon duniya.

Za a sake zama tsakanin Fubara da Wike

A wani rahoton, kun ji cewa ana rade radin shirya wani zama tsakanin gwamna Simi Fubara da aka dakatar da Nyesom Wike.

Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin za su zauna ne domin lalumo hanyar warware rikicin jihar Rivers.

Hakan na zuwa ne bayan wata ganawa da gwamnan Ogun ya jagoranta a gidan ministan Abuja domin daidaita lamuran jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »