Tsohon Gwamna, Sule Lamido Ya Fadi Makomar Najeriya idan PDP Ta Tarwatse

Tsohon Gwamna, Sule Lamido Ya Fadi Makomar Najeriya idan PDP Ta Tarwatse

  • Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya gargadi cewa ƙoƙarinraunata PDP na iya haifar da rushewar dimokaradiyya a Najeriya
  • Sule ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati, kamar yan sanda wajen raunana jam'iyyun adawa
  • Ya bayyana damuwarsa game da masu barin PDP zuwa APC, yana cewa waɗanda ke shiga APC saboda tsoro daga ƙarshe za su yi nadama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi gargadi kan ƙoƙarin da ake yi na raunana jam'iyyar adawa ta ƙasa, PDP.

Sule Lamido, wanda kusa ne a jam'iyyar hamayya, ya bayyana cewa lalata PDP na iya haifar da rushewar dimokaradiyya a Najeriya.

Lamido
Sule Lamido ya caccaki gwamnatin APC Hoto: Sule Lamido/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Lamido ya yi hasashen cewa a cikin watanni biyar masu zuwa, abubuwa masu muhimmanci na iya faruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ya kara da bayyana cewa yadda wasu daga cikin 'yan PDP ke yoyewa suna barin jamiyyar na haifar da damuwa kan makomar siyasa a Najeriya.

Sule Lamido ya fusata da masu barin PDP

Daily Post ta ruwaito cewa Lamido ya bayyana damuwarsa game da abin da ya kira wani ƙoƙarin kai hari ga jam'iyyun adawa ta hanyar amfani da dama na siyasa.

Ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati kamar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), 'yan sanda, da sauran hukumomin tsaro wajen raunana jam'iyyun adawa.

Lamido
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Asali: Facebook

Lamido ya ce:

“Dimokaradiyyar Najeriya tana bunƙasa ne ta hanyar kuzarin 'yan adawa. Idan ka lalata PDP, ba kawai ka lalata jam'iyya ba ba ne, ka dora Najeriya a kan turbar rushewa."

Sule Lamido ya caccaki Tinubu

Lamido ya zargi Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC da amfani da manyan hukumomin gwamnati domin raunana jam'iyyun adawa.

Ya ce:

“Idan APC, a matsayin jam'iyyar siyasa, tana fafatawa da PDP, hakan yana kan turba; amma idan Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin jagorancin APC, tana amfani da hukumomin ƙasa a kan adawa, hakan na da haɗari.
Ba kawai 'yan APC suke yaƙi da mu ba; gwamnatin ce da Shugaban ƙasa kansa.”
“Amfani da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomi domin tsoratar da raunana jam'iyyun adawa yana haifar da rushewar dimokuradiyya.
Wadanda ke shiga APC saboda tsoro, daga ƙarshe za su yi nadama.”

'Za a iya nasarar hadaka,' Sule Lamido

A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa domin kayar da Shugaba gwamnatin Bola Tinubu a zaben 2027.

Lamido ya bayyana cewa, ba zai yiwu a kayar da Tinubu ta hanyar fushi da son zuciya ba, yana mai cewa jam'iyyun adawa dole su hada kai da zuciya ɗaya idan suna son samun nasara.

Ya ce, PDP ce kawai jam'iyyar da ke da karfin da za ta iya dawo da mulki idan ta hada kan 'ya'yanta, duk da cewa a yanzu, ana fama da rikici da yawaitar sauya sheka zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »