Masoya Sun Daurawa kansu Aure a Kano, Sun Jefa Iyayensu a Tashin Hankali
- Wasu daga cikin yaran Kano sun yi kokarin jawo wa iyayensu magana bayan sun daura wa kansu aure da abokansu
- Aliyu Abdullahi (22) da Fatima (16) sun daura wa kansu aure a unguwar Yakasai da ke Kano, a kan sadakin N50,000
- Hukumar Hisbah ta yanke hukunci a kan auren, ta bayyana cewa bai cika sharuddan da shari’ar Musulunci ta gindaya ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu yara sun jefa iyayensu cikin tashin hankali bayan sun daura wa kansu aure ba tare da sanin iyayensu ba a Unguwar Yakasai, Kano.
Aliyu Abdullahi, mai shekaru 22, da Fatima, mai shekaru 16, sun daura wa kansu aure bayan da iyayensu sun ƙi amincewa da a daura musu aure.

Asali: Original
A cewar rahoton da Hikima Rediyo ta wallafa a shafinta na Facebook, abokan angon da na amarya Khadija sun barke da sowa da murna jim kaɗan bayan daura auren a unguwar Yakasai da ke Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Kano: Yadda matasa suka daura wa kansu aure
Wani ɗan jarida, Ibrahim Aminu Rimin Kebe, ya shaida wa Legit cewa sun yi matuƙar mamakin jin labarin daurin auren ba tare da sanin iyaye ba.
Wasu daga cikin mutanen da aka tattauna da su sun bayyana cewa bayanai sun tabbatar da cewa an daura auren ba tare da sanin iyayen kowanne ɓangare ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa angon, Aliyu Abdullahi, ya biya sadakin N50,000 ga amaryarsa Khadija.

Asali: Facebook
Wani daga cikin abokan ango – waɗanda suka taka rawa wajen gudanar da daurin auren – ya bayyana cewa sun gayyaci malami domin 'kare mutuncin abokin nasu.'
Sai dai mahaifin angon, wato Malam Abdullahi, da na amarya, sun bayyana mamakinsu da ɓacin rai bisa yadda suka ji labarin daurin auren yaran nasu ba tare da saninsu ba.
Hisbah ta soke auren matasa a Kano
Hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Birni ta soke auren da wasu yara suka daura wa kansu a unguwar Yakasai da ke Kano.
Hukumar ta bayyana cewa auren bai cika ka’idojin shari’ar Musulunci ba, don haka aka yanke shawarar soke shi.
Tuni dai Hisbah ta gayyato dukkanin ɓangarori domin sanar da su halin da ake ciki kan wannan aure.
Tun da barin, ta bayyana a matsayin aure wasan yara da aka shirya tsakanin matasa tare da taimakon abokai, kuma ya saba doka.
Ango ya rasu kafin daurin aurensa
A baya, mun wallafa cewa wani matashi da ake shirin ɗaura aurensa a Asabar, 14 ga watan Yuni, 2027, ya rasu a wani haɗarin mota da ya faru a jihar Bauchi.
Angon, mai suna Garba Mustapha, wanda jami'in ‘yan sanda ne, ya gamu da ajalinsa a garin Magama Gumau, ana dab da ɗaura aurensa da Khadija Adamu Sulaiman.
A cewar wani ɗan’uwan marigayin mai suna Shamsuddeen Hasheem Zalawah, Garba da abokinsa sun rasu sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng