Abin Tausayi: Shahararren ɗan Tiktok Ya Rasu Yana tsaka da Naɗar Bidiyo Kai Tsaye

Abin Tausayi: Shahararren ɗan Tiktok Ya Rasu Yana tsaka da Naɗar Bidiyo Kai Tsaye

  • Wani shahararren dan TikTok da aka fi sani da 'Disturbing' ya mutu a yayin da yake yin bidiyo kai tsaye a dandalin sada zumunta
  • Wata yar jarida mai bincike, Temilola Sobola, ta tabbatar da mutuwar, tana mai cewa ya rasu jim kadan bayan fara shirya bidiyon
  • Disturbing ya fadi a cikin bidiyon yayin da yake ta faɗar wasu kalamai masu zafi game da wadanda ake zargi da mutuwar Mohbad
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun ce yiwuwar shan miyagun kwayoyi ko ciwon zuciya ne suka haddasa mutuwar fuji'ar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da wani shahararren dan TikTok ya rasu.

Shahararren dan TikTok din mai suna 'Disturbing' ya mutu ne yana tsaka da naɗar bidiyo kai tsaye.

Dan TikTok ya mutu yana tsaka da bidiyo kai tsaye
Shahararren ɗan Tiktok ya shide a Lagos yayin da yake bidiyo kai tsaye. Hoto: @temilolasobola.
Asali: Instagram

Yadda dan TikTok ya rasu yana bidiyo

'Yar jarida mai bincike, Temilola Sobola, ita ta tabbatar da labarin a shafinta na Instagram inda ta wallafa faifan bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A bidiyon, an gano lokacin da dan TikTok din ya fara shidewa har ya mutu yana cikin yin shirin kai tsaye.

A lokacin da aka kawo rahoton, babu wata sanarwa daga hukumomi da ta tabbatar da ainihin dalilin rasuwar Disturbing.

Mutane sun shiga damuwa ganin mutuwa a Tik Tok

Rahotanni sun tabbatar da cewa ba a yi wata-wata ba bayan rasuwar marigayin an yi sallar jana'izarsa kamar yadda Musulunci ya koyar.

Wannan al’amari mai tayar da hankali ya karade kafafen sada zumunta inda aka nuna lokacin da ya fara rawar jiki kafin ya fadi ya mutu.

Disturbing ya shahara ne saboda goyon bayansa ga neman adalci ga mawaki Mohbad da ke zargin an kashe.

Dan TikTok ya rasa ransa yayin nadar faifan bidiyo
Har yanzu hukumomi ba su yi martani ba bayan mutuwar dan TikTok yana tsaka da naɗar bidiyo kai tsaye. Hoto: Lagos State Police Command.
Asali: Facebook

An samu mabambantan ra'ayi kan mutuwar matashin

Wasu mutane sun ce ya kasance yana zagin mahaifiyar Mohbad, matarsa, dan uwansa Adura da Liam yayin da yake watsa shirye-shiryen kai tsaye.

Wasu masu amfani da kafofin sadarwa sun bayyana cewa mutuwar na da nasaba da amfani da miyagun kwayoyi da ya daɗe yana yi.

Mutane da dama sun yi martani kan tashin hankalin da suka gani a bidiyon, suke yi masa fatan samun rahama.

Duk da haka, wasu sun nuna damuwa kan yadda yake zagin iyalan marigayi Mohbad a cikin bidiyonsa a kokarin neman adalci ga matashin mawakin da ake zargin kashe shi aka yi.

Dan TikTok ya yi ajalin kansa bisa kuskure

A baya, kun ji cewa an shiga jimami da yanayi mara dadi a birnin Virginia da ke Amurka bayan matashi mai shekaru 17 ya harbe kansa bisa kuskure ya na tsaka da daukar bidiyo.

Majiyoyi sun ce matashin dan TikTok mai suna Rylo Hunch wanda aka gani a wani bidiyo yana wulwula bindigar kafin ya saita ta a kan shi ya fadi nan take.

'Yan sanda a garin sun tabbatar da mutuwar matashi ta hanyar harbi bisa kuskure, amma ba su kama sunan Rylo Hunch ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »