'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa bayan sun farmaki jami'an tsaro a jihar Zamfara da har yau ake fama da kashe-kashe
- Tantiran ƴan bindigan sun hallaka wani jami'in rundunar Askarawan Zamfara tare da wasu mafarauta a ƙaramar hukumar Kaura Namoda
- Majiyoyi sun bayyana cewa an yi artabun ne lokacin da tawagar jami'an tsaron suka yi yunƙurin daƙile ƴan bindiga na kai hari a wani ƙauye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe wani mamba na rundunar Askarawan Zamfara (CPG).
Ƴan bindigan sun kuma kashe wasu mafarauta biyu a yayin artabun da ya faru a ƙauyen Kungurki, cikin ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ƴan bindiga sun yi artabu da jami'an tsaro a Zamfara
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, lokacin da tawagar haɗin gwiwa ta jami’an CPG da mafarautan yankin suka taru domin daƙile shirin ƴan bindiga na kai hari.
Ƴan bindigan dai ana zargin mabiya ne na wani shahararren tantiri mai suna Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Dansaudi.
Majiya daga yankin ta bayyana cewa jami’an tsaron sun shiga cikin ƙauyen ne da nufin daƙile harin da ƴan bindigan ke shirin kaiwa.
Sai dai, suna isa yankin sai ƴan bindigan suka buɗe musu wuta.
Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro
A yayin arangamar, ƴan bindigar sun kai harin kwanton ɓauna, inda suka buɗe wuta kan jami’an tsaron sa-kai.
Sakamakon haka, an kashe jami’i guda biyu na rundunar CPG da wasu mafarauta biyu nan take.

Asali: Original
Shaidu sun ce ƴan bindigar sun zo ne da yawan gaske, kuma suna ɗauke da mugayen makamai, ciki har da bindigogin AK-47.
Lamarin ya jefa al’ummar ƙauyen cikin firgici da tsoro, inda mutane da dama suka gudu suka bar gidajensu don tsira da rayukansu.
Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro inda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka.
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun nuna rashin imani, su buɗe wuta ana tsakiyar Sallah a jihar Sakkwato
- Katsina: Ƴan bindiga sun yi shigar dare, sun sace Sarki yayin wani farmaki
- Yadda yan bindiga ke tilastawa fursunoni alaƙanta kansu da Gwamna Dauda a Zamfara
Ƴan bindiga sun kai hari gidan tsohon minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a gidan wani tsohon ministan wasanni a Najeriya.
Ƴan bindigan sun kai farmakin ne a gidan tsohon ministan wasanni, Damishi Sango a jihar Plateau.
Miyagun sun hallaka ƴar uwar ministan tare da wani jami'in ƴan sanda a harin wanda suka kai a gidansa da ke ƙauyen Dalwai a ƙaramar hukumar Riyom.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng