Sarautar Kano: Muhammadu Sanusi II da Aminu Bayero Za Su Haɗu a Birnin Madina

Sarautar Kano: Muhammadu Sanusi II da Aminu Bayero Za Su Haɗu a Birnin Madina

  • Ana sa ran Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero za su halarci jana'izar Aminu Ɗantata a Madina
  • Wannan dai shi ne karon farko da sarakunan biyu za su haɗu a taron jama'a tun bayan ɓarkewar rikici a tsakaninsu a shekarar 2024
  • Muhammadu Sanusi II ya tafi Madina a tawagar gwamnatin Kano yayin da Aminu Ado ya tafi kasar Saudiyya tare da tawagarsa ta daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Madina - A karon farko tun bayan ɓarkewar rikicin masarautar Kano, Sarki na 15, Aminu Ado Bayero da sarki na 16, Muhammadu Sanusi II za su haɗu a bainar jama'a a Madina.

Matuƙar ba a samu wani sauyi ba, sarakunan da ke rikici da juna za su haɗu a wurin jana'izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina, birnin Manzon Allah SAW.

Sanusi da Aminu za su haɗu wurin jana'izar Ɗantata.
Ana sa ran sarakunan Kano 2 za su haɗu a karon farko a birnin Madina Hoto: @masarautarkano, @hrhbayero
Asali: Twitter

Leadership ta tattaro cewa rikicin sarautar Kano ya fara ne tun kimanin shekaru biyar da suka shige, lokacin da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tuɓe Sanusi II daga sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Idan ba ku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Aminu Ɗantata ya rasu a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Laraba ranar Juma'a da daddare yana da shekaru 94.

Za a yi jana'izar Ɗantata a Madinah yau

An shirya gudanar da jana'izar marigayin a yau Talata, 1 ga watan Yuli, 2025 a birnin Madina da ke ƙasa mai tsarki kamar yadda addinin Musulunci ya tanada..

Manyan mutane da suka haɗa da shugabanni da malamai ciki har da wakilan gwamnatin tarayya sun tafi Saudiyya domin halartar jana'izarsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wakilan gwamnatin jihar Kano, ciki har da Sarki Sanusi II, zuwa Saudiyya domin halartar jana’izar.

A gefe guda kuma, Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya tafi daban tare da wasu daga cikin hadimansa zuwa Madina domin halartar wannan jana’iza, rahoton Punch.

Ana sa ran Sanusi II da Aminu Ado za su haɗu

Duka Sanusi II da Aminu Bayero na ci gaba da ikirarin zama halastaccen Sarkin Kano tun bayan sauke Aminu a 2024, lamarin da ya haifar da rikici da shari’a da ake jiran hukuncin kotu a kai.

Mai magana da yawun Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya tabbatar a cikin wata sanarwa cewa Sarkin Kano na 15 ya bar Najeriya zuwa Madina ranar Lahadi.

Sanusi da Aminu Ado sun dura Madina.
sarakunan Kano, Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II za su halarci jana'izar Ɗantata a Madina Hoto: @maarautarkano
Asali: Twitter

Ya ce Sarkin ya tafi tare da tawaga da ta kunshi Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, da ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Duk da ba a tabbatar ko za su gaisa da juna ba a wajen jana’izar, wannan shi ne karon farko da ake sa ran za a ga dukkan masu ikirarin sarautar Kano a gaban jama’a.

Ɗangote ya isa Madina tare da gawar Ɗantata

A wani labarin, kun ji cewa attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ya raka gawar kawunsa, Aminu Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa birnin Madina.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gawar ta isa Madina safiyar Talata, kuma za a gudanar da sallar jana’iza a masallacin Annabi SAW bayan sallar la’asar.

Sai da aka shafe lokaci ana bin wasu ka’idoji kafin gwamnati ta amince da a birne shi a birnin mai tsarki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »