Tashin Hankali: Fada Ya Barke tsakanin Wasu 'Yan Gida 1 a Filato, An Yi Kisan Kai

Tashin Hankali: Fada Ya Barke tsakanin Wasu 'Yan Gida 1 a Filato, An Yi Kisan Kai

  • Mutum ɗaya ya mutu a Filato bayan rikici ya barke tsakanin 'yan gida daya a kan wata gona da suka gada a ƙauyen Kopkopshe
  • Shugaban karamar hukumar Mikang, Benard Alkali, ya yi Allah-wadai da rikicin, yana mai cewa yana kawo cikas ga zaman lafiya
  • Alkali ya roƙi iyalan wanda aka kashe da su guji daukar fansa, tare da alƙawarin gudanar bincike don kama wanda ya yi kisan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Rahotanni sun bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa bayan rikici ya barke tsakanin ‘yan gida daya kan wata gona da suka gada a Filato.

An rahoto cewa tashin hankalin ya faru ne a kauyen Kopkopshe, da ke Loham, cikin gundumar Tunkus, ƙaramar hukumar Mikang a jihar.

An kashe mutum 1 a Filato yayin da rigima ta barke tsakanin 'yan gida 1 kan gadon gona
Wasu manoma suna aikin noma a cikin gonarsu, a wani bangare na Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ciyaman ya tabbatar da kisa a Filato

Jaridar Leadership ta gano cewa 'yan gida dayan sun shafe fiye da shekaru biyu suna rigima kan wanda ya fi cancantar gado da mallakar gonar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Mai magana da yawun ciyaman din Mikang, Mista Nkat Joseph Lakai, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Jos.

Nkat ya ce shugaban ƙaramar hukumar, Dr. Benard Soepding Alkali, ya kai ziyarar gani da ido zuwa kauyen Kopkopshe domin tantance asarar da aka yi sakamakon rikicin, wanda ya jawo asarar rai da lalata dukiyoyi.

A yayin ziyarar, Alkali ya yi Allah-wadai da rikicin, yana mai bayyana shi a matsayin abu maras amfani da kuma abin kunya ga iyalan wanda ba za a amince da shi ba.

"Abin kunya ne rigima kan gona" - Ciyaman

Ya ce irin wannan rikici yana kawo cikas ga kokarin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin kabilu huɗu da ke zaune a cikin ƙaramar hukumar.

Ciyaman din ya nuna takaici kan rikicin, yana mai tabbatar wa al’ummar yankin cewa an ɗauki matakan gaggawa don hana rikicin ƙara ɓarke wa.

Benard Alkali ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, yana roƙon su da kada su ɗauki fansa ko ɗaukar doka a hannunsu, inda ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gudanar da bincike domin kamo wadanda ke da hannu.

“Abin kunya ne a ce yayin da gwamnati ke ƙoƙarin kare gonakinmu daga masu kawo hari, mu kuma muna kashe junanmu a kan gado. Idan ‘yan uwa sun yi fada, baƙo ke gadar filin."

- Dr. Benard Soepding Alkali.

Shugaban karamar hukuma ya roki iyalan wanda aka kashe da kada su dauki fansa
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang yayin da yake jajanta wa iyalan wadanda rikici ya shafa a jihar. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Ciyaman ya bada tallafin abinci da kudi

Shugaban ya bukaci al’ummar Kopkopshe da su zauna lafiya da juna, yana mai cewa Allah bai yi kuskure ba wajen zaunar da su tare a wuri ɗaya.

Haka zalika, ya roƙi shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki a yankin da su fara tattaunawa mabiyansu domin samar da maslaha mai dorewa.

A ƙarshe, ya ba mutanen da rikicin ya shafa kayan abinci da kuɗi, tare da alkawarin tattaunawa da hukumomin da suka dace don kawo ƙarin tallafi.

Matashi ya hallaka mahaifiyarsa a kan gado

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani matashi ya hallaka mahaifiyarsa a unguwar Umusam Ogeb da ke garin Kwale a jihar Delta, bayan sabani ya shiga tsakaninsu.

Rahotanni sun nuna cewa sun siyar da wata kadararsu tare da ɗanta ɗaya tilo, amma rabon kuɗin bai yi masa dai-dai ba, wanda hakan ya haifar da rikici mai muni.

Makwabta da suka ji hayaniya sun cafke matashin nan take suka mika shi ga ‘yan sa kai, waɗanda daga bisani suka kai shi ofishin ‘yan sanda na Kwale.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »