Matasa Sun Ƙone Ofishin NDLEA, Sun Yi Wa Mai Martaba Sarki Dirar Mikiya a Fadarsa

Matasa Sun Ƙone Ofishin NDLEA, Sun Yi Wa Mai Martaba Sarki Dirar Mikiya a Fadarsa

  • Matasan Lafiagi da ke yankin ƙaramar hukumar Edun a jihar Kwara sun fito zanga-zanga kan taɓarbarewar tsaro a yankinsu
  • Masu zanga-zangar sun kone ofishin hukumar NDLEA da ke garin tare da lalata muhimman abubuwa a faɗar Sarkinsu yau Litinin
  • A cewarsu, yanzu ba su iya barci saboda yan hare-haren ƴan bindiga, kashe-kashen rayuka da kuma garkuwa da mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Fustattun matasan garin Lafiagi, a ƙaramar hukumar Edu ta Jihar Kwara, a ranar Litinin, sun fantsama kantituna zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

Matasan sun nuna fushinsu ƙarara kan yawaitar garkuwa da mutane, kashe-kashen rayuka a hare-haren 'yan ta'addar da suka addabi al'umma.

Matasa sun ɗauki zafi kan matsalar tsaro a Kwara.
Masu zanga zanga sun kai farmaki fadar Sarki a Kwara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa masu zanga-zangar, waɗanda mafi yawanci matasa ne sun fito suna rera waƙar neman adalci da tsaro a yankinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Matasa sun fito zanga-zanga kan tsaro

Matasan sun ƙona ofishin hukumar NDLEA, sannan suka yi dirar mikiya a fadar Sarkin Lafiagi, inda suka farfasa tagogi da wasu sassan ginin.

A cewar matasan sun yi haka ne domin nuna bacin rai da suka dade suna dannewa, suna zargin gwamnati da sakaci da batun tsaronsu na tsawon shekaru.

Wani mazaunin garin Lafiagi ya ce:

"Mun dade muna kuka da ƙunci ba tare da kowa ya sani ba. Ana sace mutane kowace rana, mun rasa barci da idanu biyu yanzu, kuma babu wanda ke ɗaukar wani mataki tun daga gwamna har sarkinmu.

Dalilin da ya sa matasa ƙona ofishin NDLEA

A cewar rahoton Sahara Reporters, zanga-zangar ta biyo bayan jerin sace-sacen mutane da suka ƙara haddasa tsoro da damuwa a yankin.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da mutane uku cikin sa’o’i 12 a hare-hare biyu.

Ɗaya daga cikinsu shi ne sanannen mai sana'ar POS da ake kira Yman, wanda aka yi garkuwa da shi a daren ranar Lahadi a cikin garin Lafiagi.

Da safiyar Litinin kuma, aka sake sace Hausawa biyu a wani mummunan hari da aka kai ƙauyen Kokodo, da ke kusa da Lafiagi.

Matasa sun yi ɓarna a Kwara.
Masu zanga-zanga sun ƙona ofishin NDLEA a jihar Kwara Hoto: Kwara Info
Asali: Facebook

Mazauna garin sun koka kan matsalar tsaro

Wata majiya ta ce:

"Waɗannan fitintinu na ta kara yawa. A ranar Lahadi da yamma aka sace mai POS, yanzu kuma da safe an sake sace wasu Hausawa biyu.
"Ba mu ji komai daga masu garkuwa ba tukuna, mun sanar da jami'an tsaro abin da ya faru.

Zanga-zangar matasan ta ƙara tsananta ne bayan sace wani mai maganin ƙwari, Alhaji Chemical, wanda aka ɗauke daga gidansa da ke unguwar Taiwo a Lafiagi, da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Lahadi.

Mahara sun kashe shugaban PDP a Kwara

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe shugaban PDP na mazabar Lade tare da dansa da wani mutumi a kauyen Mari da ke jihar Kwara.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ya faru da safe a ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025.

Bayan haka kuma an samu labarin cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da wata yarinya daga rugar fulani da ake kira rugar Aiyetoro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »