NWC: Jerin Mutane 6 da za Su Iya Maye Gurbin Ganduje a Jam'iyyar APC

NWC: Jerin Mutane 6 da za Su Iya Maye Gurbin Ganduje a Jam'iyyar APC

Bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa, ana ci gaba da rade-radin waye zai gaji kujerarsa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Legit Hausa ta bibiyi muhimman sunaye da ake dangantawa da kujerar shugaban APC, musamman yayin da jam’iyyar ke kokarin sake tsari gabanin zaben 2027.

Shugabannin APC, Al-Makura, Dalori da Akume
An fara fafutakar nada sabon shugaban APC na kasa Hoto: Samuel Ordom/Hon. Ali Bukar Dalori/Senator Dr. George Akume
Asali: Facebook

Ga jerin manyan jiga-jigan da ake hasashen za su maye gurbin Ganduje:

1. Shugaban APC na rikon kwarya, Dalori

Ali Bukar Dalori, wanda ke rike da kujerar rikon kwarya, yana daga cikin jiga-jigan da ake kallon za su iya ci gaba da jan ragamar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Dalori da Ganduje
Ana ganin Dalori zai iya maye gurbin Ganduje na dindindin Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

A yayin taron farko na kwamitin zartarwa bayan murabus din Ganduje, Dalori ya bukaci hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar, yana mai cewa:

“Dole ne mu guji kalaman da ka iya haddasa rabuwar kai. Muna bukatar daidaito da haɗin kai don gina makomar jam’iyyar APC.”

Idan aka yanke shawarar shugaban APC na kasa ya fito daga yankin kamar yadda wasu ke hange, to watakila a tabbatar da shugabancin Dalori.

2.Shugaban APC: Ana yiwa Sani Musa kamfe

Wata kungiyar matasa ta North Central APC Accord ta bayyana goyon bayanta ga Sanata Sani Musa a matsayin wanda ya fi cancanta ya jagoranci APC.

A cewarta:

“Sanata Musa shi ne mafi cancanta kuma mai kawo haɗin kai. Ya cancanci jagoranci APC a wannan lokaci da ake buƙatar gyara a cikin gida.”

Sani Musa yana wakiltar mazabar Neja ta Gabas kuma yana shugabantar kwamitin kasafin kudi a majalisar dattawa.

Kungiyoyin yankin Arewa ta Tsakiya na matsa lamba a kai kujerar APC zuwa yankin su don daidaito a cikin jam’iyyar.

3. Al-Makura na iya shugabantar APC

Wata kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta bayyana Sanata Tanko Al-Makura a matsayin wanda ya dace da kujerar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ce:

“Mun gudanar da dogon nazari da tuntuba a yankinmu, kuma Al-Makura ya cika ka’idojin da suka dace da shugabanci.”
"Al-Makura yana da ƙwarewa sosai, kuma yana da kusanci da tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, wanda dukkaninsu daga Nasarawa ne."

4. Ana son Akume ya zama shugaban APC

Bayan murabus din Ganduje, wasu ‘yan siyasa da kungiyoyi na matsa lamba ga Sanata George Akume da ya bar kujerar SGF don jagorantar APC.

Duk da haka, Fadar Shugaban Kasa ta karyata rade-radin cewa Akume ya sauya matsayi kamar yadda aka rika yada wa a farko.

Sanata George Akume da Abdullahi Umar Ganduje
Wasu na matsa lamba kan Akume ya maye gurbin Ganduje Hoto: Senator Dr. George Akume, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Hadimin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya ce:

“Labarin da ke yawo cewa an maye gurbin Akume ba gaskiya ba ne. Ana neman a yada jita-jita ne kawai.”

5. Joshua Dariye a shugaban APC

Tsohon Gwamnan Filato, abokin siyasa na Tinubu, Joshua Dariye na cikin mutanen da ake hango zai iya hawa kujerar shugabancin APC.

Business Day ta rahoto cewa shi da Shugaba Tinubu sun kasance abokan aiki tun daga lokacin da suka zama gwamnoni a 1999 har zuwa 2007.

Masu nazarin siyasa na ganin Dariye na da kyakkyawar dama, musamman domin taimaka wa APC su karfafa matsayinsu a yankin Arewa ta Tsakiya.

6. Wasu na goyon bayan Yari a jam'iyya

Kwanan nan jaridar The Sun ta rahoto cewa wasu matasa a Arewa maso yamma suna goyon bayan Abdulaziz Yari ya zama sabon shugaban APC.

Tun a 2021 aka ji wasu 'ya 'yan jam'iyya mai mulki sun fito sun goyi bayan tsohon gwamnan na Zamfara ya jagoranci majalisar NWC ta kasa.

Yayin da APC ke fuskantar 2027, tambayar da ke gabanin ita ce, ana fafutakar dauko wanda zai iya jagorantar jam'iyyar domin kai wa ga nasara.

Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

A wani labarin, kun ji cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, domin mayar da hankali kan lafiyarsa.

Shugaba Bola Tinubu ya ba Hon. Ali Bukar Dalori, mataimakin shugaban jam’iyyar a Arewa umarnin karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar na riko.

Gwamnonin jam’iyyar karkashin sun yi maraba da wannan sauyi, suna mai cewa saukar Ganduje na nuna cigaban cikin gida na jam’iyyar a tsarin shugabanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »