Atiku Ya Tabo Maganar Daina Siyasa, Ya Ce zai Koma Jami'a bayan Ritaya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zai koma jami’a bayan ya yi ritaya daga harkokin siyasa
- Ya furta haka ne a Abuja lokacin da yake jawabi a bikin yaye dalibai na shekarar 2025 a makarantar Pacesetters’ a Abuja
- Atiku, wanda ya kafa American University of Nigeria (AUN), ya jaddada muhimmancin zuba jari a ilimi da ci gaban ɗan Adam
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana shirinsa na komawa karatu a jami’a lokacin da ya yi ritaya daga harkokin siyasa.
Atiku Abubakar ya yi magana yana mai cewa ilimi ne mabuɗin bunƙasa ƙasa da dukkan wasu harkokin cigaba.

Asali: Facebook
Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya yi bayani a taron yaye dalibai da aka yi a makarantar Pacesetters’ a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Atiku da ya kafa jami’ar American University of Nigeria (AUN), ya faɗi hakan ne a ranar Lahadi a Abuja, cikin jawabin da ya gabatar a makarantar Pacesetters’.
Atiku zai koma jami'a bayan gama siyasa
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaben 2023 ya nuna sha'awar komawa jami'a, inda ya ce:
“Ko bayan ritaya daga harkokin siyasa, ina fatan komawa jami’a.”
Atiku ya roƙi gwamnati da masu ruwa da tsaki su tallafawa makarantu da kuɗin gudanarwa, da tsara manhajar da ke ƙarfafa kirkire-kirkire da fasaha a tsakanin ɗalibai.
Da haka ne Atiku ya jaddada cewa cigaban Najeriya na hannun manyan masu ilimi da masu kishin ƙasa, wajen ba da dama ga kowa ya sami ingantaccen karatu.
Atiku ya yaba wa makarantar Pacesetters
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yabawa Kenneth Imansuangbon, wanda ya kafa Pacesetters’ Schools Abuja, bisa jajircewarsa wajen samar da ingantaccen ilimi ga matasa.
Tribune ta wallafa cewa ya ce:
“Babu wani zuba jari mafi alheri fiye da a fannin ilimi, domin yana ba mutum damar zama injiniya, likita ko duk wata sana’a da mutum ya zaɓa.”
Atiku ya taya daliban da suka kammala karatu a shekarar tare da yin kira ga hukumar makarantar da ta faɗaɗa ta zuwa matakin jami’a.

Asali: Twitter
Atiku: Ilmi shi ne mabuɗin cigaba
A jawabin nasa, Atiku ya ce ilimi ne mabuɗin da zai buɗe ƙofa ga ƙasarmu, ya sa turbar bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa ta bunƙasa.
Ya jaddada cewa ƙasa mai ilimi kaɗai ce za ta guji rikice-rikice da ja-in-ja, inda ba za a iya juya al’ummarta ba zuwa harkokin siyasa marasa kan gado.
Ya ce:
“Ilimi yana tabbatar da haɗin kan ƙasa, kwanciyar hankali da ci gaba,”
Atiku ya yi ta'aziyyar Aminu Dantata
A wani rahoton, kun ji cewa, Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
A sakon ta'aziyya da ya fitar, Atiku Abubakar ya ce lallai Najeriya ta yi babban rashin dan kishin kasa mai habaka tattali.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wa gwamnatin Kano da masarautar jihar jajen rasa babban dan kasuwa, Aminu Dantata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng