Sojojin Najeriya na Shan Wiwi da Kwayoyi kafin Su Fita Fagen Daga? Gaskiya Ta Fito

Sojojin Najeriya na Shan Wiwi da Kwayoyi kafin Su Fita Fagen Daga? Gaskiya Ta Fito

  • Birgediya Janar Baba Omoparioala ya ce sojojin da ke barikin sojojin Katsina ba sa bukatar wiwi ko ƙwayoyi kafin su fita fagen daga
  • Kwamandan ya yi watsi da ra'ayin cewa ƙwayoyi suna ƙara kuzarin sojoji a fagen yaƙi, yana mai cewa horo ne mabudin nasara
  • Hukumar NDLEA ta yi gargadin cewa shan ƙwayoyi yana kai ga ta'addanci, fashi da maki, da sauran miyagun laifuka a cikin al'umma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Kwamandan Birgediyar soji ta 17 da ke Katsina, Birgediya Janar Baba Tunde Omoparioala, ya ce sojojin da ke ƙarƙashinsa ba sa tu'ammali da ƙwayoyi.

Birgediya Janar Omoparioala ya jaddada cewa sojoji ba sa buƙatar tabar wiwi, ko kowane nau'i na miyagun kwayoyi don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kwamandan Birgediyar soji ta 17 da ke Katsina ya ce sojoji ba sa bukatar wiwi ko kwayoyi don yin aiki
Hafsan sojojin Najeriya tare da tawagarsa yayin rangadi a wani daji. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kwamandan Birgediya ta 17 ya yi watsi da ra'ayin da ake yaɗa cewa shan kwayoyi yana ƙara kuzarin sojoji a fagen yaƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a Katsina a wata lacca mai taken "Wurin aiki da al'umma marasa tu'ammali da kwayoyi" wanda hukumar NDLEA ra shirya.

Shin soja yana buƙatar wiwi don yin aiki?

Birgediya Janar Omoparioala ya ce:

"Shin mu ba marasa tsoro ba ne? Shin ba mu da dakakkiyar zuciya ne? Me ya sa soja zai ce yana buƙatar wiwi don ya yi aiki? Wannan maganar banza ce."
"Ɗaya daga cikinsu ya gaya mani, 'Ranka ya dade, ina buƙatar wiwi don in yi aiki.' Na amsa masa, 'Kada ka sake yi mun wannan banzar maganar. Idan sai ka sha kwayoyi za ka yi aiki, me ya sa aka horar da kai a matsayin soja?'"

Leadership ta rahoto kwamandan ya jaddada cewa horo, jajurcewa da kuma yakini su ne ke tasiri a aikin soja ba wai shan kwayoyi ba, yana mai cewa:

"Mun gudanar da samame ba adadi, kuma mun yi nasara ba tare da shan wiwi ba. Ya kamata a tura duk wani soja da ke iƙirarin akasin zuwa ganin likita, don a dora shi a kan magani."

Kwamandan ya kuma buƙaci hafsoshin sojoji da su kiyaye doka, yana mai cewa, "Idan kuna tsoron sojojin da ke kasan ku, to ba ku da wani dalili na jagorantar su."

Hukumar NDLEA ta ce shan miyagun kwayoyi ne ke kai ga taaddanci, fashi da makami da sauran laifuffuka.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA). Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Illar shan miyagun kwayoyi ga al'umma

Mataimakiyar shugaban sashen kwayoyi na NDLEA, Zainab Ibrahim, wacce ta gabatar da babban jawabin laccar, ta danganta shan miyagun kwayoyi da ta'addanci, fashi, da laifukan tashin hankali.

Zainab Ibrahim ta ce:

"Babu wanda zai yanke kan ɗan adam ba tare da ya bugu ba. Babu wani mai hankali da zai yi hakan."

Ta yi gargaɗi cewa shan miyagun kwayoyi yana lalata daidaikun mutane, iyalai, da cibiyoyi, kuma ta ƙi amincewa da uzurin cewa rashin aikin yi yana ba da hujjar shan miyagun kwayoyi.

Sojoji sun kama masu kai wa 'yan bindiga kwayoyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta cafke mutane biyu da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi.

Rundunar ta bayyana cewa an kama mutanen a hanyar Kekeno zuwa Cross Kauwa a jihar Borno kuma a kwato kwayoyi da tabar wiwi.

Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, kakakin rundunar MNJTF ya kara da cewa sojojin sun ceto wasu mata uku da jaririn a yayin atisayen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »