1447AH: Gwamna Radda Ya ba da Hutu don Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci
- Ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina sun samu hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1447 bayan hijira
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya ayyana Juma'a 27 ga watan Ƴunin 2025 a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekara
- Hakazalika ya buƙaci mutanen Katsina da su gudanar da addu'o'i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da Najeriya baki ɗaya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da hutu domin shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1447 bayan Hijira.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya ayyana ranar Juma’a, 27 ga watan Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira (AH).

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Faskari, ya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Gwamna Dikko Radda ya ba da hutu
An bayar da hutun ne domin bai wa ma’aikatan gwamnati da mazauna jihar damar yin murna da kuma yin tunani kan muhimmancin wannan rana mai tarihi a addini.
A cikin sanarwar an bayyana cewa Gwamna Radda ya miƙa sakon taya murna da fatan alheri ga dukkanin Musulmi a faɗin jihar da ma Najeriya baki ɗaya bisa samun damar ganin shigowar sabuwar shekarar Musulunci.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da fahimtar juna, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya jaddada cewa ba za a iya samun ci gaba mai ma’ana ba sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamna Radda ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da ayyuka masu amfani da za su inganta rayuwar jama’a.
Haka kuma, Gwamnan ya sake jaddada kiransa ga manoma da kuma waɗanda suka amfana da tallafin noma na gwamnati da su yi amfani da taki, taraktoci da sauran kayan noma da aka raba domin ƙara yawan amfanin gona musamman a wannan damina da ake ciki.

Asali: Facebook
Gwamna Radda ya yi kira ga manoma
Hakazalika ya kuma buƙaci manoma da su guji shiga dazuka, hanyoyin kiwo da filayen kiwo na makiyaya ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamna Radda ya kuma yi addu’a domin dorewar zaman lafiya, hadin kai da wadata a jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Aliyu Hashim ya shaidawa Legit Hausa cewa hutun da gwamna Radda ya ba da abin a yaba ne kuma mutane za su ji daɗin shi.
"Eh wannan hutun ya kamata tabbas, kuma kusan mu yanzu a Katsina ya zama al'ada ana badawa a duk shekara."
"Muna fatan a maida shi a ƙasa ma baki ɗaya ana badawa a duk shekara."
- Aliyu Hashim
Gwamnan Kwara ya ayyana ranar hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya ba da hutu don shigowar sabuwar shekara musulunci.
Gwamna Abdulrazaq ya ayyana ranar Alhamis, 26 ga watan Yunin 2027 a matsayin ranar da ma'aikata ba za su je wurin aiki ba don murnar shigowar sabuwar shekarar ta 1447 bayan Hijira.
Hakazalika ya yi kira ga mutanen jihar da su gudanar da addu'o'i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng