Gwamnan Taraba Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamna? An Ji Gaskiyar Zance
- Wasu rahotanni da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa gwamnatin jihar Taraba ta naɗa sabon mataimakin gwamna
- Gwamnatin ta fito ta musanta batun cewa ta naɗa mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Hamman-Adama Adamu a muƙamin
- Ta bayyana cewa har yanzu Alhaji Aminu Abdullahi Alkali shi ne mataimakin Mai girma Kefas Agbu a jihar Taraba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta yi magana kan batun naɗa sabon mataimakin gwamna.
Gwamnatin ta bayyana cewa iƙirarin da wasu mutane ke yi na cewa ta naɗa mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Hamman-Adama Adamu, a matsayin sabon mataimakin gwamna, ba gaskiya bane.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta ce kwamishiniyar yaɗa labarai ta jihar Taraba, Zainab Jalingo, ta bayyana hakan yayin da take jawabi a wajen wani taron manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Me gwamnatin Taraba ta ce kan naɗa mataimaki?
Gwamnatin jihar ta jaddada cewa babu gurbi a ofishin mataimakin gwamna, kuma Alhaji Aminu Abdullahi Alkali har yanzu shi ne sahihin mataimakin gwamnan jihar Taraba da aka zaɓa a bisa ƙa’ida.
Gwamnatin ta buƙaci al'umma da su kwantar da hankalinsu tare da dogara kawai da sahihan bayanai daga kafafen sadarwa na gwamnati.
"Gwamnatin Taraba ta lura da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda ke cewa mai girma gwamna, Dakta Agbu Kefas, ya nada Alhaji Hamman Adama a matsayin sabon mataimakin gwamna na jihar Taraba."
"Wannan ikirari ƙarya ne, cike yake da ruɗani, mugunta ne kuma ya kamata al'umma su watsar da shi gaba ɗaya."
"Muna so mu fayyace cewa babu wani gurbi a ofishin mataimakin gwamna. Har yanzu Alhaji Aminu Abdullahi Alkali shi ne sahihin mataimakin gwamnan jihar Taraba da aka zaɓa a bisa tsarin doka."
- Zainab Jalingo

Asali: Twitter
Babu shirin maye gurbin Alhaji Aminu Alkali
A cewar gwamnatin, tsarin maye gurbin mataimakin gwamna kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, a bayyane yake, yana buƙatar bin matakan majalisa da tsarin doka, kuma babu wani irin shiri ko tunanin aiwatar da hakan a halin yanzu.
Gwamnatin ta ƙara da cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen aiwatar da nagartaccen shugabanci, ba tare da ta baro jita-jita marasa tushe ta ɗauke mata hankali ba.
A kwanakin baya ne dai mataimakin gwamnan ya dawo birnin Jalinho bayan ya kwashe lokaci yana jinya a asibiti.
Alhaji Aminu Alkali dai ya kwashe kusan wata huɗu baya cikin taraba.
An daina jin ɗuriyar mataimakin gwamnan Taraba
A wani labarin kuma, kun ji cewa fargaba da rashin tabbas ta mamaye zukatan mutanen jihar Taraba sakamakon rashin ɗuriyar mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali.
Rashin ji daga wajen mataimakin gwamnan tare da ƙasa gudanar da ayyukan ofis ya janyo ana shakku dangane da lafiyarsa.
Sai dai, wasu rahotanni sun bayyana cewa mataimakin gwamnan yana fama da matsalar bugun zuciya kuma ya kwanta jinya a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng