'Ba abin Kunya ba ne': Farfesa da Ke Sayar da Kayan Miya Ya Fadi Sirrin Rayuwarsa
- Farfesa Nasir Hassan-Wagini na jami'ar Katsina ya bayyana dalilin da ya sa aka ga yana sayar da kayan miya duk da matsayinsa
- Malamin jami'ar ya shaida cewa mahaifinsa manomi ne, kuma ya koyi noma tun yana yaro, don haka ne yake noman kayan lambu yanzu
- Maimakon jiran aikin gwamnati, Farfesa Hassan-Wagini ya bukaci matasa da dalibai su cire kunya su fara yin sana'o'in hannu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Farfesa Nasir Hassan-Wagini na sashen kimiyyar halittu a jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU), Katsina, ya fadi dalilinsa na shiga sana'ar sayar da kayan miya.
Farfesa Nasir wanda ke nomawa da sayar da kayan miya, ya shawarci ɗalibai da matasa da su rungumi sana'o'in hannu maimakon jiran aikin gwamnati.

Asali: UGC
Dalilin Farfesan na sayar da kayan miya a Katsina
Farfesan ya bayar da wannan shawarar ne ranar Litinin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a wata kasuwa a Batsari, jihar Katsina, inda yake sayar da kayan miya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Farfesan ya bayyana cewa manomi ne ya haife shi, ya girma a matsayin manomi, kuma ya fara harkar kasuwancin kayan gona tun yana ƙarami.
A cewar malamin, labarinsa da kuma sana'ar kayan miya da yake yi ya bazu ne bayan jami'ar UMYU ta kara masa matsayi zuwa farfesa.
"Kira na ga masu NCE, Diploma, da Digiri shi ne su cire kunya, su fara ƙananan sana'o'i a yankunansu maimakon zama babu aiki," in ji Farfesa Hassan-Wagini.
'Matasa su yi sana'a, su bar zaman banza' - Farfesa
Ya ƙara da cewa:
"Ni farfesa ne a fannin albarkatun shuke-shuke a UMYU, ina so matasa da ɗalibai su buga misali da ni, duk da matsayi na, ina yin ƙananan sana'o'i irin wannan."
"Abin da ke da muhimmanci shi ne abin da kake yi wa al'umma. Don haka, kada ku ci gaba da zama a gida kuna zaman banza idan ba ku sami aiki ba, ku fara da ƙananan sana'o'i kamar wannan."
Farfesan ya shawarci matasa da dalibai da shiga harkar noma da sauran ƙananan sana'o'i don zama masu dogaro da kai mai makon yin kaura zuwa wasu ƙasashe.
Shaidar al'umma kan Farfesa Hassan-Wagini
Ɗaya daga cikin maƙwabtansa a kasuwar, Uzairu, ya bayyana cewa suna jin daɗin kasancewa da farfesan a kasuwar.
Ya bayyana farfesan a matsayin amintacce, mai tawali'u, kuma mai kirki a mu'amalarsa da mutane.
"Muna girmama shi kuma yana girmama mu. A gaskiya, mutumin kirki ne wanda ya san yadda zai yi mu'amala da kowane nau'i na mutane," in ji Uzairu.

Asali: UGC
Farashin kayan miya a kasuwar Batsari
Daily Nigerian ta ruwaito cewa farashin buhun albasa mai nauyin kilo 100 a kasuwar yana kai N65,000 ko sama da haka, ya danganta da ingancinsa.
Rahoton ya nuna cewa ana sayar da buhun busasshen barkono ja mai nauyin kilo 100 a kan N115,000, yayin da buhun busasshen tumatur mai nauyin kilo 100 ya kai N60,000.
A hannu daya kuma, ana sayar da buhun busasshen tattasai mai nauyin kilogram 50 a kan N100,000 a kasuwar ta Batsari.
An kuma samu labarin cewa a cikin 'yan watanni masu zuwa, manoman rani za su fara girbe tumatur, barkono ja, albasa, da sauran kayan lambu.
'Noma tushen arziki' - Mustapha Gama
A zantawarmu da matashin dan kasuwa kuma manomi, Mustapha Muhammad Yusuf Gama daga Kano, ya ce mutane ne ke raina noma, musamman na lambu.
A cewar sa:
"Mutane suna dauka cewa duk mai yin noma talaka ne, ko kuma ba zai yi arziki ya hau manyan motoci ba. Abin da suka kasa gane wa shi ne, an daina irin noman kaka da kakanni, yanzu noman zamani ake yi.
"Yanzu ba noman a ci abinci ba ne, noma ne na neman kudi. Shi ya sa za ka ga an bullo da tsare-tsaren noma na zamani, irin su greenhouse, soiless farming, ma'ana noman da ba a bukatar kasa wajen yin sa."
Mustapha Gama ya ce ganin Farfesa Hassan-Wagini yana sayar da kayan miya bai kamata ya zama abin kaskanci ba, domin shi ne ke noma kayansa, yana sayarwa.
Ya ce:
"Manomi mai dabara shi ne wanda zai noma kuma ya sayar da kayansa a farashin masu sayen dai daya. Saboda ya fi riba a kan farashin sari. Kuma shi kayan lambu ai lokaci gare shi.
"Ana noma shi da sayar da shi cikin watanni shida bayan ruwa ya ja. To ka ga a wannan lokacin ne za ka zama ba ka da hutu. Amma yanzu akwai noman lambu na zamani, a gidanka ma za ka iya yi, idan kana da fili."
Sabuwar matsala ta kunno kai a jami'ar Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an sake ɓarkewa da rikicin shugabanci a jami'ar FUDMA bayan wasu sun ƙi amince wa da sabon shugaban jami’ar da aka zaɓa.
Wasu daga cikin ’yan takarar kujerar sun zargi shugaban jami’ar mai barin gado da amfani da matsayinsa don fifita ɗan takarar da yake so ya samu shugabanci.
Farfesa Sadiq Radda ya kai ƙara ga ministan ilimi, yana zargin cewa an cire sunansa daga jerin ’yan takara ba bisa ƙa’ida ba, yayin da Farfesa Usman Dustinma ya ce an nuna son kai a zaɓen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng